Ina gode ma Yesu Christi domin wannan baiwa da kuma kalmomin da ya ba ni domin ku.
Ceto ba aikin mutum ba ne. Dukan mu ke nima ga zuwan wurin ALLAH ne. Ba za mu kuma bar ALLAH’N nan ya cece mu ta yanda ya gamshe shi.
Gaskiya ba ya cikin wunin mu; ni ba gaskiya ba ne, kuma kai ba gaskiya ba ne. Sanan ya na da amfani mu zo ga gane juna. Idan na ji gaskiya a wurin ka sai in yadda, kuma idan ka ji gaskiya a wuri na sai ka amince. Uba daya muke da shi, Kuma niyan sa ne dukan mu mu zo ga sami ceto.Ta tarayya ba za mu yi wannan tafiyan garesa ta wurin gaskiya.
Sai wani lokacin da ina kan rubutu nan (na turanci), sai ya kuma fito mun a alfahariya da cewa; “Ni ne gaskiya! Ku na bambanta a kan me ne bayan da ni ne gaskiya, kuma gaskiyan nan kauna ne”. Toh a nan mun gan cewa duka wani abu adini-mutum ne. Ainayin ALLAH ma na shi ne kauna.
Toh ku ji tunanin Ruhu mai tsarki ma ni; Abun halitan mu ko kasan halitan mu ba abun gaskiya ba ne da wai za ce wai akwai wani sujada ko irin sujada na gaskiya. Wato idan mun ce wai akwai sujada na gaskiya, wato daga ayukoki ko halayen mu, toh mu na iya fadi da wai mutum fari ma na iya ce wai shi ne gaskiya, wato, mutum baki zai je wuta kenan? Kokuma mutum mai harshen Ibrananci sai ya ce wai shi ne gaskiya, wato mutum mai harshen Larabci zai hallaka kenan?
Mu halitan mu shine domin mu yi shaidan gaskiya ta wurin kalman ALLAH, ama ba wai ma na ba ne mu yi ta halita gaskiya. Kuma yanda na fada gaskiya kauna ne. Duk wani abu da zai kawo bambanci ba gaskiya ba ne, kuma ba daga wurin ALLAH ba ne, domin niyan ALLAH ne mutum su kasance a tarayya. Adini duk halitan mutum ne bisa na shi tunanin gaskiya. Toh mun gan da cewa adini ya na kawo bambanci ne bisa yanda kowa na da nasa tunanin gaskiya, ama kuma gaskiyan kauna ne.
ZUWAN YESU.
Toh zuwan Yesu ma na kenan, domin ya amsa da kuma warware damuwan kai da adini. Toh ta hakan ne ba shi da jiki, wato kowa ma na iya kasance jikin sa. Komai shi ne ama shi ba komai ba ne. Bakin mutum shi ne, kuma farin mutum ma shi ne, ama shi ba su ba ne. A hakan ma mai durkusa da gwiwan shi a kasa ma adu’a shi ne, kuma mai durkusa da goshin sa ma a kasa shi ne, ama shi ba su ba ne. Ta wurin sa komai dai dai ne ama ba gaskiya ba ne, wato kuma shi ne adinin yahudawa kuma shi ne adinin Musulunci ama su ba shi ba ne, dalilin da kowa ma na da na sa irin nuna sujada, ama kuma kadda wani ya dauki na sa hanyan ne gaskiya. An halice mu alloli ne ta yanda mu na da na mu halaye dabam da wayensu.
MUTUMIN YESU.
Misali, da wai za yi aure, sanan wai kowa ya sa riga kala ja. Toh, ta wurin Yesu, ta yanda ba shi da jiki ko mutuntaka, shi ba zai sa riga ja din nan ba ta dalilin, me ne hadin riga ja da aure? Auren ba za ta yihu ba da wani kalan riga? Ama shi kuma bai hana sa jan kaya din nan ba. Ama idan za’a sa jan kaya, toh mu san ba gaskiya ba ne, domin auren tana iya yuhu ko da wane irin kaya. So kadda wani ya kore wani daga auren domin bai sa jan kaya ba. Ma wanda sun ce wai za su sa jan kaya, su sa, ama su iya jumre ma wanda ba su sa jan kaya din nan ba, domin jan kayan ba tabacin aure ba ne. Idan wanda sun sa jan kayan za su yi fushi da wanda ba su sa jan kaya ba, sai ma kadda su sa wai doka ne wai wani ya sa jan kaya, domin ba wani abun da ya hada jan kaya (ko wani musaman kalan kaya) da aure.
Ama dai kuma, ta wurin zuciyan Yesu, doka ne a kai na (mai bin Yesu) in sa jan kayan nan, domin salama ta kasance. Duk ba komai a wurin idan na sa jan kaya din domin ba zai dauki komai daga jiki na ba.
Ama ainayin mutumin Yesu shi ne, shi ba ya halita irin dokokin da ba su da muhimmanci; ba ya halita dokokin da ba gaskiya ba. Toh kiran masu bin sa kenan; Kadda mu zo ga halita hanyoyi bisa ganin mu sai kuma mu sa shi wai doka ne a kan mutani yayen da ba gaskiya ba ne. Ma masu bin Yesu, su yan al’ada ne, ama ba yan adini ba, ama kuma yancin al’ada nan ba na yin ayukokin duniya ba ne. Masu bin Yesu ba yan adini ba ne, su yan al’ada ne, wato ko wane hali na iya kasance da su ama kuma halayen nan su tabata ta kauna, da huta da rayuwan tsarki, da rashin alhakin laifi. Ama kuma su yan adini ne, domin ana iya ce da ayukan mutum daya ma adini ne ta yanda adini daga halin da tunanin mutum ne.
Dalilin da Yesu ya kasance Magana da kowa kenan, misali; mata yar Samaritan. Sanan mun gan yanda abun ya zama da mamaki ma almajirai’n sa (John 4:27). Toh ta kuma haka ne ya kawas da adinin yan israelawa, ta yanda ya nuna da wai kowa ma na iya samu ceto, domin da shi bisa Almasihu ya zo ya kasance a adinin yahudawa da kuma halin adinin su, toh da mu wanda ba aifuwan yahudawa, da na mu hallaka kenan.
Toh a hakan ne kuma muna iya ce da wai ya kasance ba shi da jiki, ta yanda ya na iya dangantaka da kowa, kuma bai bar halin yan yahudawa ya yi mulki a kan sa ba.
Domin sun dauka su ne gaskiya, wato ceto su ne. Ama mun gan Yesu a yayin da shi yana iya kasance da ko wane irin mutum domin shi ne gaskiya, kuma domin gaskiya ba ya cikin mutum, kuma mutum ba gaskiya ba ne, wato kowa ma na iya kasance a gaskiya kenan.
Toh ku gane Yesu; shi bai hana adini ba, ama ta wurin sa, ba halin masaman da wai ceto ne. Ko wane hali, idan ya kasance ta zuciyan dan tunkiya ko da rashin laifi ko alhakin laifi, ALLAH ba ya fushi da halin ba.
Musulunci ta zo ga ganewa; ba halin da wai ceto ne. Ko wane hali na iya kasance adini ko sujada ma ALLAH idan ta kasance ta wurin kalman ALLAH, wato kauna, da rai, da tsarki, da rashin alhakin laifi, da hutu. ALLAH ya halice mu alloli, wato kowa da na sa irin halin. Toh a haka ne mu na faranta zuciyan ALLAH, ta yanda mutani dabam suna iya kasance a bambantaka su kuma yi zama tare.
Wato, ta wurin zuciyan yesu, bisa dan tunkiya ko mai rashin alhakin laifi, ana iya samu mai Magana da kuma mutum shiri shiru, wato kadda mai maganan nan ya yi magana da mumunan zuciya, kuma kadda ma mutum mai shiru din nan ya kasance a shirun sa da mugunta a zuciyan sa. Toh a hakan ne mu na zo ga godiya ma bambancin mu, sanan sai mu gode wa ALLAH ta wurin junan mu. Kowa ma jiki ne ma Yesu, bisa kalman gaskiya. Na mu shi ne mu kasance a yanci ama ta zuciyan Yesu Christi.
Toh a hakan ne ana iya samu masu durkusa da gwiwa a adu’a, da kuma masu bauta Kaman yanda kuna yi, kuma ana iya samu ma su zama su yi adu’a (II Samuel 7:18), har da ma su tsayawa. Ama dai zuciyan shi ne ‘a cikin niya da kuma gaskiya’ (John 4:23), toh kalman gaskiya mana kenan. Abun tabata sujadan mu ga ALLAH shine idan mun kasance a cikin gaskiya, ama ba yanayin bautan mu ba.
YESU YA SHAIDA MUN MUSULUNCI.
Wani rana, yayan da ina makaranta, sai Yesu ya shaida mun Musulunci ta wai; Su mutani ne ma su son fadi, wato a adu’a, ama ba swa kula su ji, mutani ne masu son aikatawa kuma ba swa so su saurara, toh ta yaya ne za su sani?” Kuma kuwa ya na son ya yi magana da ku, ama ku ko kun riga kunyi karfi a halin ku.
Akwai kuwa wani lokacin da ina kurkusa da Musulunci sosai, har ina tsayawa har dare domin in kalla wa’azi na Ramadan na su. Sai na kuma ji wani imam ya ce; “idan ALLAH na so ya gafarce mu zunubai’n mu, yana iya fadawa ne, sannan kuma ya faru, ama ba sai da kashe Yesu Christi ba”. Toh har tunanin nan ya fara zama a zuciya na domin na gan ya je daidai da lojik na ‘allah’. Sanan a lokacin sai Ruhu ya amsa mun da cewa “da ba mu gan gafaran nan ba, ya za mu sani? Sai ta yane za mu karbi gafaran nan?
Toh ku ji; Yesu ne sani da wai ALLAH ya gafarta mana zunubai’n mu. Mu kuma karbi alherin nan ga nuna ta ma junan mu da kuma ma masu zunubi.
YESU BISA KALMAN ALLAH KUMA KALMAN GASKIYA.
DOKA.
Mene doka? Daga ina ne doka yakan fito?
Na fari, doka hali ne. Ama ana iya ganin doka bisa kalma (ko kalmomi) da ke kawo zaman lafiya sakanin mutani. Ama ma masu bi, muna samu dokokin mu daga halin ALLAH ne, kuma dokokin nan ne kamata halayen mu. Kuma domin an halice mu ma alloli daga abun ko kasan halitan mu, dalilin da muna rayuwa ta halin ALLAH kenan bisa dokokin mu. Kuma ta kiyaye dokokin nan ne kalmomin dokokin su na halice mu Kaman ALLAH da kuma yayan ALLAH.
YESU CHRISTI.
Sa’alin da doka halin ALLAH ne, idan wani ya yi ma laifi sai ka kashe shi, toh ka gan kai ma ka karya wani doka kenan; dokan kauna da kuma daya a cikin dokoki guda Goma, wato kada mu kashe wani. Ko kuma wani ya ma sata, sai ka je ka kuma rama ta zuciyan ramako, toh wanan ramakon ya kai ka ga karye ita dokan da baka ji dadin bayyanuwar sa a kan ka ba. In yanka maganan, ramako na kai mutum, ko na sa mutum a saman dokan shi ma, domin dokan daga halin ALLAH ne, kuma idan kayi ramako, toh ka ba laifi wa mutumin ALLAH kenan. Toh Yesu Christi ma na kenan a Matthew 5:38-48.
Toh, mun gan dalilin da Yesu ya zo mana bisa kauna kenan, kuma dalilin da ya kawas da horo da kuma hukuncin kisa wanda yayan israela suke amfani da shi bisa dokokin ‘adinin ALLAH’ kenan. ALLAH kauna ne, kuma kaunan’nan ne ya kuma zama mana dokan hali, dalilin da mu ma yana gafarta mana idan munyi laifi ma sa. Toh idan na kaunace ka, bazan ma sata ba. Ama sa’alin da na ma sata, dokan kuma kauna ne, domin dokan halin ALLAH ne kuma ALLAH ba ya canzawa (Malachi 3:6). Domin idan ALLAH na canzawa, ya kuma nuna ma na da cewa ALLAH ba shi da hali, kuma shi mutum ne domin mutani ne kowai suna bambanta a lokotai.
Ama domin Yesu ko ALLAH ya ce wai idan anyi man laifi sai muyi gafara, ba wai ya bari ayi ta cuce mu ba, kokuma, ya sa dokan, wato yana bukatan zunubi domin a kiyaye dokan kaunan sanan ya samu daukaka ba. Halin nuna kauna ma wanda sun ma laifi na kawo su ka canzawa sosai, wato halin kaunan nan na kawo masu shegen kunya har ga tuba.
Ama kuma akwai dalili da ALLAH ya kasance kauna a fiskan zunubi, kuma ya ba mu ita wanan halin mu kiyaye bisa halin mu. Dalilin shine GANEWA. Toh wannan aikin Ruhu mai tsarki ne ya kawo mana ga ganewan nan.
- Na daya, Ta wurin Ruhu mai tsarki, muna zo mu gane da cewa masu laifi ko zunubi mutani ne wanda basu da kalman ALLAH, ko alherin ALLAH. Wannan ya kamata ya mosa mu ga tausayi ne masu, dalilin da idan Yesu ya soko yanzu, nasu wurin zuwa halaka ne ba mulkin sama ba, domin basu da shaidan Yesu Christi, wato shaidan kalman ceto ba.
- Na biyu, ramako baya canza mutum, Kuma baya kawo mutum ga tuba. Idan mutum ne da laifi, idan ka rama, yakan ki tuba, dalilin da wai ka rama. Sai wanan dalilin ya kwantar da zuciyan sa ga yanda zai amince yayi laifi har ga niman tuba.
- Na uku, idan mutum yayi niyan ma mugunta, toh ka san ba abun da zai iya kawo sa ga tuba inba ALLAH ba. Sanan da wai zaka rama, wanan zai kawo har ga fada ne ama ba tuba daga wurin sa ba. Canza mutum aikin kalman ALLAH ne da Ruhun ALLAH, domin sune suke kawo ma mutum sanin laifi da kuma karbin laifin sa, ramako da horo ba swa taba kawo ga tuba, har ga niman gafara a wurin ALLAH.
- Ramako bisa wai dokan ALLAH yakan nuna cewa bamu yadda da zaman ALLAH ba, kuma ba mu yadda da wai ALLAH zai ba ma kowa ladan sa ba, dalilin da munso mu samu rabon mu kenan a fiskan laifi’n.
DOKOKIN KAUNA NA YESU (Matthew 5).
Kalma kauna amsa ne ma damuwa kuma shi mafita ne a damuwan. Wato, ta wurin kauna, baza mu aikata laifi ma juna ba, ama idan wani yayi mun laifi, toh, mafitan kauna ne. Dalilin shine rashin sani ko alheri ta wurin mai laifi din. Domin sa’alin da laifi ya na iya canza mu, wato ya dauki kwanciyan rai’n mu, Yesu ta wurin kauna, ya kawo mana yanda za mu kasance a cikin kwanciyan rai din idan aka aikata mana laifi. Barawo ya zo kowai domin ya yi mana sata, kuma ya kasha mu, kuma ya lalatar, ama ni na zo domin ku sami rai, kuma ku same shi cikeke (John 10:10). Toh, mun gan idan wani yayi mana laifi, wanda aka masa laifin ne yafi jin zafin, kuma laifin yafi dauki hankalin sa. Ama ta wurin gafara da kuma kin kula da wanan laifi din, mu kan kasance da kwanciyan rai’n mu. Niyan shaitan shine ya gan yanda zamu amsa laifi da laifi, domin muma mu kasance da zunubin aikata halin da ba kyau din a cikin sunan ramako da kuma mu yi raye da bacecen zuciya, ama ta wurin zuciyan Yesu, ta wurin kauna, za mu kasance da adu’a ne ma ma su ma na gafara (Matthew 5:43-48), dalilin da suna rayuwa da rashin alherin ALLAH da kuma kaunan ALLAH, da kuma rashin sani kalman ALLAH, kuma ta wurin haka, za mu kasance da yanci.
Dokokin Yesu na kauna (Matthew 5:38-41), wanda wai “idan a mare ka a kumatu daya, ka kuma juya dayan domin a kuma mari”, kokuma da wai, “ma wanda zai caje ka a kotu ya karba rigan ka, toh ya kuma samu alkyabbaa din”. Da Kuma “duk wanda zai sa ka dole kayi tafiya mil daya, toh ka je da shi mil biyu”. Duka wayenan kalaman ke fiskacen zuciyan yesu bisa wanda bai san wani abu laifi ba. Bai karba zaman laifi ba. Kalaman na sun fiskance zuciyan sa bisa mutum da bai waye da laifi ba, bai bar laifi har ga sammun wurin zama a zukatan shi ba, domin masu yin laifi mutani ne wanda ba su da alherin ALLAH, toh bai kamata mu bar irin wannan mutanin ko halayen su canza mu ba.
Ama a hakan, wanan ba bayannuwan Yesu Christi mana ba kenan. Shi bai yi bukatan laifi domin ALLAH ya sa mu girmama ta wanan bangaskiyan ba, wato, ALLAH ba ya bukatan ayi mana laifi sanan domin mu bi kalman jumrewan sa. Shi ya zo bisa kauna ne ma ma su bin sa, wato, a sakanin su, ta zuciyan kauna, ba wanda zai mari wani, ko ya kai wani kotu, ko ya sa wani dole domin yayi wani dogon tafiya da bai so ba. Zamu kasance daya ta zuciyan kauna wa junan mu, kuma idan wani ma ya yi laifi, sai ya nima gafara, sanan ta wurin ganewa, wanda aka masa zunubin zai yafe. Aikin ma su zuciyan Yesu ne su zama ma su wakilcin Yesu ta wurin nuna gafara ma ma su zunubi, toh a hakan ne mu firistocin ALLAH.
Ama yanzu kalmonin sun zama dokan salama. Domin ramako ke kawo ga fada ne. Kalmomin kauna ko jumrewan nan suna halice mu a kamanin ALLAH idan mun za ma ma su jumrewa yayan da an ma na laifi. Domin da Kalman ALLAH ya zo gareni, ya kuma ce mun “kazo ga samin kanka a salaman da zai kasance idan ka jumre a gaban laifi”.
Sai na kuma gan wani abu, Yesu ne kalman gaskiya, kuma ya na da yanci ya ki kashewan da za ma sa. Da ya so na yaki ne, da ya yi, domin shi ya kasance a gaskiya ne kuma ya na da masu goyon baya, ama sai kuma ya bari an kashe shi. Sai Ruhu ya sani na gane da cewa da ace Yesu ya yi yaki da yan majalisan, toh na daya; da har yau za samu cingaban wannan yakin sakanin masu bin Yesu da kuma masu goyon bayan majalisan. Na biyu; Yesu da zai halita ma ma su bin sa halin fada ko ramako ko yaki.
Kuma sa’alin da Yesu ya bar rayuwan tsarkin sa domin ceton mutum, bai yi tunanin kansa ba, wato tsarkin sa, ama sai ya gan cewa mu a duhun mu ke bukatan sa-shi haske. Ya ji laifin zunuban mu, bisa shi ne amsan zunubai’n mu. Toh, a hakan ne shi ya zama dan ragon hadaya, domin da bai jumre a gaban zunubai’n mu ba bisa kalman ALLAH, da ya yi abin da kamata ne, wato, kashe ma su laifi idan kayi zunubi, toh, da babu mutum mai rai yanzu. Toh kun gan, ta halin jumrewa, mu ma mu na iya zama yan ragon na hadaya, domin ta wurin hadayan kai namu ne salama zai kasance.
“NI NE UBANGANGIJI, ALLAH’N KU”.
Mun gan cewa kalman nan na gaya mana cewa sunan mai fadawa Ubangiji ne ba ALLAH ba. Kalman ya ce “ni ne Ubangiji, Allahn’n ku” ba “ni ne Ubangiji, ALLAH” ba, wato shi ne Allah’n mu, ta yanda shi ne ya gyara mu a kamanin sa, wato ta tsarin mu a mike da kuma kamanin hali domin mu samu tarayya da kuma abokantaka da ALLAH. Ta farko, ALLAH ya yi niyan ganin halin sa a abun halitan mu, wato kasan halitan mu, dalilin da ya yi amfani da halin ko kalman sa, wato Yesu Christi domin halitan mu. Toh a hakan ne Yesu Allah’n mu ne, ta yanda shi ya gyara mu kuma muna samu halin mu daga wurin sa ne, ama kuma ba shi ba ne ALLAH.
Abun kaman yanda iyayen mu suka haife mu ne;
- Na daya, Su ne mahaifuwan mu, ama kuma su ma aka haife su ne, toh a hakan ma yayanda Yesu ne ya halice mu, ama shi ma halitan ALLAH ne.
- Na biyu, duk biyayya da za mu musu, ya kamata ya tafi daidai da nufin ALLAH ne, to a hakan ma yesu ya kasance Ubangijin mu domin ya jagorance mu ta hanyar ALLAH ne.
- Kamata su ne fiskan ALLAH mana, wato muna zo ga sanin ALLAH ta wurin su da kuma ta ganewan su, toh hakan ne Yesu Christi mana, ta yanda shi ne kalman ALLAH. Ama ba shi ba ne ALLAH, ama kuma kamin ya yi mana Magana akan ALLAH bisa kalman gaskiya ko kalman ALLAH, domin ya waye da ALLAH ne. Ta yanda Yesu ya kasance kalman gaskiya a mutuntaka, kamata mu san akwai abun da ya bambanta shi da sauran mutani. Eh, kwarai ya kasance mutum a duniyan nan, ama kuma ya zama mutum ne, ama farkon sa ba a mutuntaka ba ne, farkon san na allahntaka ne (John 1:1-3).
A kalma “Ni ne Ubangiji Allah’n ku, toh Yesu ya na wayas da kansa ma su israelawa da kuma mana ne, wato shi bisa Ubangijin mu, ama kuma mahalicin mu.
Ubangiji ba ALLAH ba ne kuma ALLAH ba Ubangiji ba ne. Wato abun Kaman kin kujeran firayam minista domin akwai kujeran shugaban kasa. Ko kuma zabi ka kira tabacecn kujeran firayam minista, kujeran shugaban kasa. Yesu bisa Ubangiji bai ce wai shi ne ALLAH ba, domin yanda ya faru da Yusufu wanda ya zama gwamnar dukan kasa Masar (Genesis 41:40, 41, 43) ama kuma ba shi ba ne sarkin kasa ba, ko kuma da Daniel wanda aka zamar da shi masaraucin kasar Babyla (Daniel 2:48), wanda kuma dukan kai na lardunan suna kawo repotu masa ne, ama kuma ba shi ba ne sarkin kasa. ALLAH ALLAH ne, kuma ALLAH ba Ubangiji ba ne domin ALLAH ya yi sama da kujeran Ubangiji. Yesu ne Ubangiji ta yayan da shi ne ya gyara halita kuma shi ne na wakilce ALLAH a gaban halitatun sa, wato shi ne (Yesu) na aikata nufin ALLAH a gaban halitatun sa.
KALMAN GASKIYA.
“Shine Isa, yaron Maryamu – kalman gaskiya wanda suke shawarwari a kai” (QS. Maryam 19 verse 34).
“Ka ambata lokacin da malaiku sun ce, ya Maryamu, kwarai ALLAH ya baki kyaun bushara na kalma daga wurin sa, wanda sunansa zai zama Almasihu, Yesu, yaron Maryamu- rarrabe a wanan duniya da kuma bayyan wanan rayuwa da kuma a cikin wanda za’a kawo su kusa da ALLAH”. (QS. Aal-i-Imraan 3 verse 45).
- Yanzu, ta yayane Yesu kalman gaskiya ne a Musulunci? Ina kuma kalman gaskiyan nan a Musulunci? Kuma ta yaya ne kunyi ko kuna biyayya ta kalman?
- Yesu bisa kalman ALLAH- Toh, ba ya zama kalmomin sa ne zamu bi ba? Ba shine kalaman sa ne nufin Allah ba? Ba shine kalmomin sa ne gaskiya da kuma ceto ba? Ba nufin shine; idan mutum yayi mana Magana, maganan ba dokan ALLAH ba ne a kan mu, amar maganar Yesu shine gaskiya, kuma dokar ALLAH ne a kan mu ba?
- Ta wurin kalmomin nan ne muna karba sanin zunubi kuma muna karbi tuba, kuma muna sanin alherin ALLAH gare mu-domin kalaman nan ne sun nuna mana da cewa ba mwa tafiya daidai da ALLAH kuma da kamata da mun mutu ne, ama ta wurin kaunan ALLAH, yayi mana gafara ta wurin nuna mana alherin sa yanda ya tura mana kalmomin nan ta wurin Yesu Christi domin mu gyara tafiyan mu da shi. Ama sa’alin da Musulunci bata waye da kalmonin yesu ba, ta yaya ne suna sanin zunubi? Kuma sa’alin da Muhammad ya kuma tayar da dokon ramako wanda Yesu yazo ka kawas da shi, ta yaya ne kuna biyayya ga ALLAH?
- Yesu bisa kalman ALLAH ba wai muna aikata niyan sa (Yesu) bane. Karbin Yesu Christi domin mu karbi sakon ALLAH, ama ta wurin sa (Yesu) ne. Kin Yesu ba kin Yesu bane. Kin Yesu kin ALLAH ne (John 12:44-50). So ba yanda zaku karbi yesu, ku tabatar da ALLAH’N sa sai ku kuma ki biyayya ta wurin sa (Yesu). Karbin Yesu domin ku karbi ALLAH’N Yesu din ne, kin Yesu kuma shine kuyi musu ma wani ALLAH dabam. Domin halin ALLAH baze iya kasance kauna da horo a lokaci daya ba.
- Mutum bazai iya halita ko gyara adinin ALLAH ba ta ganin sa ba. Duk wani gyaran da zamuyi, dole ne sai ya je daidai da nufin ALLAH. Toh, duk wani adini na ALLAH ko ma ALLAH shine Yesu Christi, domin shine (Yesu) gyaran adinin israelawa, ta yanda ALLAH ne ya turo sa da sakonin masu da kuma mana. Baza mu iya ba wa ALLAH ganin mu bisa wai adinin sa ba. Toh ta yayane Musulunci ta kira kanta yan bauta ma ALLAH, sanan kuma su ne suna halicin yanda zasu yi wanan bautan? Ta yaya ne mutum zaiyi bauta ma ALLAH inba ta wurin hanyar ALLAH ba? Ai ALLAH ne zai nuna mana wannan hanyar bautan domin mu yi biyayya ga hanyoyin nan. Toh Yesu Chriti bisa kalman ALLAH mana kenan. Ta wurin sa, wato ta wurin kalmomin sa ne muna bauta ma ALLAH. Toh idan mutum ya halite nasa hanyoyin bauta ma ALLAH ta ganin sa, mun san ko yana faranta zuciyan ALLAH ko ba ya faranta zuciyan sa?
- Ta dalilin mene kun karbi cewa yesu ne kalman gaskiya ama kuma ba kwa biyayya ga kalaman sa? Kuma idan kunce wai yesu yazo ya cika Torah, dalilin mene kun kira sa kalman gaskiya idan kwa kalmomin nan, wato dokokin Torah sun kasance gaskiya kamin shi? Wato ta yaya ne shi kalman gaskiya, kuma ta yaya ne kalmomin sa gaskiya ne, kuma mene karyan? Domin idan kun ba da gaskiya wai Yesu ne kalman gaskiya kuma kalman ALLAH, toh, kun ambata bambancin sa da kalmonin Torah kenan, Kuma sa’alin da kun ambata wai shine Almasihu ama sai bakwa kiyaye kalmomin sa, wato kun ba laifi ma ALLAH kenan, wato dalilin mene ya bukance gafara da kauna a kan yayan sa, ba ramako ba? Wato kun nuna sani da iko fiye da ALLAH kenan, da shike yayi Magana a Yesu Christi, ama sai kunki ku karbi kalman nan.
- Kalaman ne ta kawo mana dokan yafewa, a yanda muma ALLAH yana yafewa mana. Wato, ta dokan nan ne munzo ga ainayin sanin ALLAH, da cewa bashi bane ya bukance dokokin hukuncin kisa wanda yayan isaraela sunyi amfani da shi bisa dokokin adini da kasa.
- Kalman ne ta kawo mana Allantaka ta yanda ALLAH yake. Wato, ta yanda adini ta kwace kai na mutani ga iya nuna gafara, toh Yesu yazo ya bamu wanan yancin da sakewa da iko na nuna gafara akan laifofin mutani.
- Kalman ne ta nuna mana cewa ALLAH baya tambaya Adini ah wurin mu, Ama ke bukata rayuwa ta kamar yara ko yan tunkiya.
RUHU MAI TSARKI.
Kuma kwarai mun ba ma Musa Torah, kuma mun bi bayyan sa da manzzani. Kuma mun ba ma Yesu, Yaron Maryam, hujjoji masu sarari, mun kuma tallafa masa da Ruhu mai tsarki. Ama ba shine da wai kowane lokaci wani manzo ya zo gare ku [Ku yaran Israela] da abin da rayukan ku basu so ba, wai kun kasance da girman kai? Sai kuma wani kungiyan manzzanin kun ki su, sai kuma kun kasha wayensun su”. (QS. Al-Baqara 2 verse 87)
- Ama, da shike kun tabatar da cewa akwai Ruhu mai tsarki, don mene ba kwa nima kuyi shedar sa a musulunci?
- Domin shine tunanin Allah mana.
- Shine ke bamu sarkakewa.
- Shine ke bamu shedan yesu Kristi ta wurin nasaran sa a kan zunubi a duniyan nan. Toh a hakan ne shi mai ceton mu, domin muna shaida da kuma amfani da nasaran sa ne ta wurin namu ayokokin.
- Kuji; mutum abun ganewa ne ba sani ba. Aka gyara mutum bisa rayuwan sa ta wurin Ruhu ne am aba kalma ba, dalilin da an kira Yesu kalman ceto kenan- domin dama ALLAH yayi niya mutum yayi rayuwa ta Ruhu ne ba kalma ba, domin duka sanin mu don ya kai mu ga ganewa da kuma shaida ne. Toh kuji; Mutum baya iya gane kalma har ga aikata shi ba, inba ta ganewa ta Ruhu ba. Kalman tana iya ce kauna, ama mutum baya iya san ta yayane zai nuna kaunan nan, kuma wane lokaci ne zai nuna wannan kauna din ba, wato a cikin salama ne ko a fiskan laifi ne. Misali; Doka na biyu ta ce, “kada ku gyara wani abu mai wani kamani wanda ba rai, ko wani abu mai kamanin abun da na sama ko kasa, ko wanda na karkashin kasa, ko wanda na cikin ruwa a karkashin kasa. Kada ku bauta masu ko ku musu wani hidima, domin ni Ubangiji Allah’n ku dan kishin ALLAH ne, kuma ina sa hukuncin zunubin iyaye a kan yaran su har ga zamanin uku da hudu ma wanda sun ki jini na”. Ama sai kuwa Musulunci ta ke bauta wa kaaba, ama sai kuma su ce wai ba bautan gumaka bane suna yi. Mun gan da cewa suna da kalman, ama kuma Ruhu mai tsarki bai ganar da su bisa kalman doka na biyu dinan ba. Doka na biyu dinan tana gaya mana da cewa ba abun da zai iya saya a madadin ALLAH, ba abun da zai iya wakilce ALLAH. Shi ya halice duniya ama kuma ba abun da zai iya wakilce sa. SHI, kalman SHI ne, kuma abun da na iya wakilce sa kenan, kuma kalman nana ne doka na biyu. Duk wani gunki da zamu gyara daga hanun mu ne, ama kuma akwai mai iya gyara kalman ALLAH, kokuma akwai mutum da shine ya gyara kalman ALLAH? Zabi ka bauta ma wani abu dabam da kalman ALLAH, shine ka kawas da shi kalman ALLAH’N kenan domin kalman ne kowai na nuna ALLAH a sakanin mu.
Kunce wai kaaba gidan ALLAH ne, ama damuwan dutse ne a ciki, wato kaaba’n ke rufe dutse ne. har da wai ana sumbata dutsen da kuma yi masa kuka. Ama kuma doka na biyu ke gaya mana da cewa ba abu mai iya wakiltar ALLAH ba. Idan kun ce wai bauta ma dutsen nan yanda ALLAH na gwada biyayyan ku ne, ba ta wurin kalman sa ba ne mutum ke masa biyayya? Ba kalman sa ne shi ba? Ama kuma sai mutum ya ki kalman, sanan wai ya nuna biyayya ma ALLAH ta wurin sumbata dutse?
Abu daya ne kowai ya na iyar wakilce ALLAH, kuma shine kalman sa, wanda yake gaya mana mutumin ALLAH. Kuma ta wurin kalman nan ne muna ma ALLAH sujada, ama ba ta wurin wani abu kuma ba.
Jikunan mu ne gidan ALLAH, domin ALLAH na kasance ta wurin kalman sa da Ruhun sa a zuciyan mu ne.
Musulunci tayi yaki da masu bauta ma gunki da abubuwan da ba rai, ama sai kuma me ne bambancin su da wayanan mutanin idan suma ke bauta ma dutse har ga sumbata dutse? Ama sai a ce kunyi yaki domin girmama ALLAH, ama kuma wai ku ne kuna rege mutumin ALLAH ta wai dutse ne na wakilce sa?
Kokuma yanda doka na shida ya ce kadda mu yi kashi. Ama sai kuma Muhammed ya kasance a wannan halin ne har ga girman Musulunci. Toh, idan ka kashe wani, yaya ne zai zo ga tuba ko ga karbin ALLAH daga sanin sa? ALLAH bai dauki yanci zabin mu ba, ama sai mutum ne sai ya kuma kafa da wai bin ALLAH dole ne? Toh mun gan duk wanan halayen sun bayanna a cikin Muhammed domin ba shi da Ruhu mai tsarki da zai bayanna ma shi nufin ALLAH. Duka wannan ne muna ce da su bangaskiyan kai, domin bangaskiyan ALLAH na cikin alheri da rai da kauna ne, kuma a cikin wayanan ne mutani masu zunubi sun zo ga tuba, kuma suna zuwa ga tuba. Sanan kuma idan ka je ka aikata naka bangaskiyan, sai kuma mutani su ki ALLAH ta yanda halin ka mumuna ne.
YARON ALLAH.
“Sun ce, ALLAH ya dauki yaro. Daukaka ne SHI! Komai na mulkin sama da mulkin kasa nasa ne. kuma duka suna da yawan biyyaya gare sa” (QS. Al-Baqara 2 verse 116).
Toh ku gani, hanyar ALLAH ba na mutum ba ne. Kada mu dinga amfani da hanyar mu muna tunanin ALLAH go fadin ALLAH. Yesu yaron Allah ne ta wurin aikata nufin Allah. Niyan Allah ne ya sauko duniya domin ceton mutum, kuma domin ya yi nasara a kan zunubi- kuma hakan ya yi. Toh a hakan ne shi yaron Allah, kuma idan mu ma munyi nufin nan da ya kawo mana ta wurin kalmomin sa, a hakan muma mun zaman yaran Allah. So mu yaran ALLAH ne, ama ta wurin Yesu Christi, wato ta wurin aikata kalmomin sa.
Sahih Bukhari 7.18 yayi ruwaito: Shi Annabi ya tambaye Abu Bakr ma hanun ‘Aisha a aure. Sannan Abu Bakr ya ansa “Ama ni danwan ka ne”. Sai Annabi ya kuma fadi, “kai danwa na ne a cikin Adinin ALLAH da kuma ta wurin takkadan sa, kuma ba laifi idan na aure ta (Aisha).
Toh, ta yaya kun ki cewa mu ba yaran ALLAH ba, sai kuma Muhammed ya kuma ce shi danwan Abu Bakr ne ta wurin Adinin Musulunci? Iyayen su guda daya ne? Ama ta wurin haka, mu yaran ALLAH ne idan mun yi rayuwa ta biyayya ga kalmomin ALLAH, kuma ta haka ne Yesu ya zama yaron ALLAH- ta wurin biyayya ga niyan ALLAH, ta yanda ya (Yesu) bar rayuwan tsarki da ya kasance a ciki a mulkin sama domin ceton mutum, ama ba ta wurin jimayi ba. Tunannin da wai ALLAH ba shi da mata da wai zai haifu yaro, tunannin mutum ne. Toh kuma mun san hanyoyin ALLAH ba hanyoyin mutum ba. Na mu aikin shine mu dinga barin Ruhu mai tsarki yana bishe mu da koyas da mu ta abubuwan ALLAH, ama ba wai ma na mu kai namu tunanin ga sanin ALLAH ko ga gane ALLAH ba. ALLAH ba mutum ba ne da wai ya na harkan jinni. SHI ALLAH ne kuma shi cikeke da bangaskiya ne, kuma bangaskiyan nan ne kalmomin sa, kuma shine mun ji ta wurin yesu Christi ta yanda kun bada gaskiya da wai shi ne kalman ALLAH.
ALLANTAKA NA YESU CHRISTI.
“Sun kasance da rashin yadda sun da sun ce ALLAH ne Almasihu, Yaron Maryam, bayyan da Almasihun ya ce, ku yayen Israela, ku yi sujada wa ALLAH, Ubangiji na da kuma Ubangijin ku. Kwarai, wanda ya hada daidai da ALLAH wani, toh, ALLAH ya haramta shigan aljannan sa, kuma wurin kasancen sa shine wutan. Kuma ba masu taimako ma azzalumai”. (QS. Al-Maaida 5 verse 72)
- Toh ba muma litafi ya kira mu alloli ba? (psalms 82:6)
- ‘Allah’ bisa kalma ke iya nufi abu mai iya zabi.
- ‘Allah’ bisa kalma ke iya nufin mai dubi (responsibility), ko mai gado.
- ‘Allah’ bisa kalma na iya nufi kai, wato wanda na da abu har ga iya bayaswa.
- Kadaincin mu ma na nuna mu alloli ne.
- Allantaka kuma na iya nufin ‘mai kamar da Allah’. Toh, kamanin mu da Allah ke zuwa bisa abun da shi ALLAH yake. Shi kauna ne, kuma idan mun nuna kauna, muma ana iya ce da mu alloli. Kuma yanda Yana nuna gafara, muma idan mun nuna gafaran nan, toh ana iya ce da mu alloli. Ama allantakan mu dai ke zuwa daga wurin ALLAH UBA ne, ta wurin dokokin sa a Yesu Christi. A takaice, duk abin da na iya rayuwa ta kalmomin ALLAH, allah ne, domin kalmomin ALLAH ne abun da ALLAH ya ke.
- Ba wai mun ce shi ne (yesu) ALLAH na farko ko ALLAH UBA ba, Ama shi Allah ne ta wuraren da na gaya ma ku, wato ta wurin zabi, ta wurin gado, kuma ta wurin kama da ALLAH bisa dokokin ALLAH, kuma shi ne ya yi halita ta wurin nufin ALLAH UBA.
Abun tunannin mu ne. kalma ba shine ganewa ba. Kalma daya ke iya nufin abu dabam dabam ma kowa. Kowa ke iya ganin kalma bisa gwanintan sa ne. Yayan israelawa da sun kashe Yesu wai domin ya ce shi yaron ALLAH ne sunyi amfani da gwanintan su ne sun hukunta Yesu. Ama ita kalma “yaro” ke iya nufi rainon yaro ne, wato ALLAH ya raina Yesu bisa yaron sa ta wurin biyayya ga nufin sa. Yanda Yesu ya kira kansa yaron ALLAH ama ku kun doki cewa ALLAH na da mata, kuma mu mun gane cewa ta wurin dangantaka ne.
Rashin kasancewan su da ku a cikin Ruhu mai tsarki ne ya kawo ga ganewan nan. Da sun bi dokokin ALLAH da ya turo ta wurin manzzanin sa, da Ruhu ya ba su shaida da wai su ma yaran ALLAH ne. Alhaki laifi ne ya kawo har ga kashen Yesu, domin shi bai taba gaya ma su da wai ALLAH na da mata ba. Mu yi hankali da yanda muna amfani da namu ganin ko gwaninta muna tunanin abubuwan ALLAH. Yayan israelawa sun dauki kalman “yaro” ta yanda kalman ya kasance ne, kuma halin nan ne musulunci sun zo ga koya. Yanda na fada, ALLAH ba mutum ba ne, mu kuma bar harkan ganin ALLAH ta wurin harkokin mu.
Almasihun, yaron Maryamu, manzo ne kowai; har an kasance wayensu manzzani kamin shi. Kuma har maman sa mai goyon bayan gaskiya ne. Har sun saba cin abinci. Ku gan yanda muka bayanna masu Alamomin; sai ku gan yanda suke a yaudara.
- Mun kuma gan tunanin Muhammed a gane Yesu bisa Allah a nan; yanda wai “sun saba cin abinci”. Muhammed yana iya zama da gaskiya, ama mun gan da cewa tunannin sa kenan bisa abun da ALLAH yake, kuma abun da kamata ALLAH yake. Na ce ‘kalman yana iya zama gaskiya’ dalilin da ba wanda ya taba ganin ALLAH ko ya waye ALLAH da wai zai yi mana shaida ko ALLAH yana cin abinci ko babu.
Idan mun hada da wanna ayan, zamu gan yanda ya dinga ambata “Almasihu, yaron Maryamu” (a cikin quran), wato wai Yesu dan haifuwa ne. Ama, abun na nan Kaman yaro ne wanda baban sa sarki ne, sanan shi ne yarima. Sai ya kuma samu kansa a soja. Toh, mun san da cewa a aikin soja, ba’a bin girman mutum sai dai girman su na soja din. Toh mun gan da cewa ikon sarautan shi a sojan bashi da amfani, wato bazai iya umurce wani a soja din ba ta wurin ikon sarautan shi. Ya kuma samu mutani daga gidan talakoki ma a kan sa. Kwarai Yesu mutum ne a duniyan nan, ama ainayin abun da yake, wato kalman ALLAH tun daga farko bai canza ba. Ruhu ya halice sa kalman ALLAH din ne mana, wato Ruhu ya halice sa kalman bangaskiya ta yayan da ya zo domin ya kawas da zunubi ne. Ama ainayin kasancewan sa kamin zunubi tsarki ne ba bangaskiya ba. Bangaskiya na nufin bayannan mu a fiskan zunubi, ama rayuwan tsarki na nufin rayuwan da ba zunubi gabaki daya. Sanin sa, wato, asalin sa ko farkon sa na Allahntakaka ne ba mutuntaka ba (John 8:42, 17:5, 16, 18, 21, 22). Asalin Yesu na Allahntaka shine a John 17.
YIN MA KALMAN SUJADA/ BANGASKIYAN KAI/GANI.
Su, wato yayan israelawa sun yi sujadan dokokin ALLAH ne ta wurin tunannin su, kuma ta hakan, ba su fiskance ALLAH ba, domin ALLAH mai gafara ne domin mutum ya zo ga tuba. Ama idan an ji ma mutum ko an kashe shi, mutum din ba ya iya zo ga tuba, kuma a hakan, ALLAH ne na rasawa domin niyan sa ne mutum ya zo ga tuba, wato, ya zo ga nuna nasara akan halin da ba kyau dinan, wato ya daina mumunan halin.
Yesu ya ba mu allantaka daga abin da ya ke, domin mun rasa wanan allantakan ta wurin adini. Hukuncin kisa ko horo ke zuwa daga wurin mutum ne bisa tunanin sa ga abun da Allah ya ke a fiskan zunubi, sanan kuma ya yi sujada ga dokokin nan. Ama ALLAH ke ba mu lokaci da alheri domin mu zo ga tuba ko nuna nasara a kan zunubin nan. ALLAH na rasawa idan an kashe mutum bisa zunubin sa kuma bai zo ga tuba ba ko bayyad’da shedan nasara a kan wannan halin zunubin, domin niyan sa ne mutum ya zo ga tuba. Kuma bayannanan Yesu mana kenan, wato ya zo ga kiran ma su zunubi ga tuba (Luke 5:31-32).
Mutum zai zo ga tuba ta yaya ne indan mu kashe shi? Kuma zai gane kaunar da kuma alherin ALLAH ta yaya ne idan mun kashe shi ko mun ji ma sa.
Duk wani irin tsarin doka da ba kauna ba da kuma alheri ba, basgaskiyan kai ne ko bangaskiyan mutum ne, kuma ALLAH ba ya rikodin wannan tsarin dokan bisa bangaskiya mai kyau ma ma su aikata hukunci. Kuma domin shi (ALLAH) ya riga ya ce shi na sa tsarin doka a fiskan laifi shine kauna da alheri, toh duk wani tsarin doka da ba kauna ba ya zama rashin biyayya. Niyan ALLAH ne da cewa kowa yayi rayuwa da yanci, sa’alin duk wanda za su kiyaye dokokin sa, su yi ta wurin zabi, kuma wanda ba za su kiyaye dokokin nan ba su kuma yi ta wurin zabi. Duka hukunci na sa ne, kuma zai ba wa kowa ladan sa ranan karshe. Kada mai zunubi wai ya na ma ALLAH hukunci bayyan da shi ma da ALLAH ya bi na ji ma masu zunubi ne, da shi ba shi da rai har ga wai yin ma ALLAH hukunci.
Yakan faru wai mutum mai yin hukuncin shi ne dalilin da wai wani ya yi zunubi, ama wai shi zai yi hukuncin zunubin. Misali; idan ALLAH ya ce mu ba ma wanda ba su da shi, sai kuma ba mu yi ba, sannan mutum din ya ji yunwa har ga sata. Toh dokan ku ya ce wai a yanka hanun mai sata; ama rannan sharia, ALLAH na iya ba ma mai sata dinnan aljanna domin ya san da mutum din ya kasance da abinci, da ba zai yi satan nan ba. Ama ku da doka ya ce idan mutum ya ji yunwa sai ku ba sa ama kun ki, kungan ku ma kun karya doka, kuma dalilin karya dokan ku ne ya kai ga satan mutum din can. Toh, kun gan ALLAH na iya ce kaddaran ku wuta ne.
Ya na kuma iya kasance wai baba bai koya wa yaron sa dokokin ALLAH ba, sannan kuma yaron nan ya je ga aikata zunubai din, toh mun kuma gan da cewa akwai laifin baban a nan. Toh, ta dalilin haka ne mutum bai kamata, kuma bai isa yin hukunci ma ALLAH ba. Idan mutum ya yi sata, sanan sai ya mayas da abun da ya sata, kuma sai su shugaba su kawo sa ga tuba. Ama idan sata din nan na abinci ne-domin mutum yaji yunwa, toh wannan abun kunya ne ma shugabancin domin ya nuna kasawan su ga ciyar da kowa. Sai kuma dukan su, wato, shubancin da kuma mai sata din su nima gafara a wurin ALLAH, sai kuma su gyara kasawan su din. Domin da’a ce wanda ya kamata ya bayas ya bayar, da wanda bai kamata ya rike fiye da ya ke bukata ba, da wai wani zai yi sata ne? kokuma da baba ya koyas da yaron sa a hanyoyin ALLAH, da yaron nan zai kasance mai aikata laifofi ne? Toh, mun gan kowa ma na iya kasance da laifi konda ba shi ba ne ya aikata mumunan zunubin. Dalilin da duka hukunci na ALLAH ne, kuma na Yesu ne, domin shi ne kalman ALLAH dinan.
KIRAN MU GA ZAMA FIRISTOCI.
Ta wurin nuna gafara, Yesu ya kawo ma mutum Allantakan da adini ta sace. A adini, wanda an masa laifi- shi shaida ne kowai da cewa an karya dauka, ama adini ba ta ganin sa bisa wanda aka azabtar. Ama Yesu mana, ya zo ya ba ikon gafara ma wanda aka azabtar dinan. Yesu ya kuma gane da zafin zunubin da an ma sa, domin kalman da an karya wanda adini ta sa dokan hukuncin kisa bisa shafin su, shi ne, wato Yesu Christi ne, dalilin da yana da iko ya ba ma mutum ikon gafara a kan kalman da aka karya din kenan.
Ama shi, ya kasance, wato aifuwan sa bisa kalman ALLAH mana ne domin mu yi shaidan sa ga junan mu, ga samun zaman lafiya. Wato kuma shi ne dokan mu.
Ta zuwan sa, ya zamar da mu firistoci, wato ya ba mu ikon gafara akan dokokin nan da an karya, wanda ya kawo har ga laifi ya kasance ko faru. Misali; shi ne doka ko kalma ‘kadda ku yi sata’, ama dokan nan ya kasance ma na ne, kums idan mun yi shaidan kalman nan, zamu yi zaman lafiya. Ama dokan halin ALLAH ne mana, toh, kun gan shi ne halin ALLAH dinnan ko kalman nan. Adini kuma ta ce, wanda ya karya kalman nan, kaddaran sa hukuncin kisa ne. Ama da ya soko mana, ya kuma zaman da mu firistoci a kan kalman nan, wato, ya ba mu iko a kan kalman nan, ko mu ce, ya ba ma wanda aka azabtar ikon gafara a kan kalman sa’alin da an yi mishi sata. Toh mun gan shi ne ya mayas da mutum kai ta wurin da ya kira ko wane dayan mu ya zama firist, wato, mai nuna gafara a madadin sa kuma a kan sa- shi bisa kalman kenan.
Ta kuma haka ne ya kawas da adini, domin ya kawo kai da kuma yankin shawaran hukunci ma wanda aka azabtar, wato ya kwace wannan yankin shawaran daga wurin alkalai ko gwamnatin adinin. Sai kuma ya canza dokan hukuncin kisan nan zuwa kauna, dalilin da mu ma masu laifi ne wa ALLAH, kuma ta wurin kauna mana ne ALLAH ya na yafe mana. A hakan ta wurin kauna, wato gafara, muna samu kamani da ALLAH.
Kuma dokan gafaran nan doka ne ma yayan ALLAH domin abun da ALLAH ya ke kenan, kuma bai kamata mu fiskance wani doka da ba kauna ba. Toh, a nan ne mutum ya samu iko, wato kai. Toh, bai kamata wai Musulunci da wai su na shaidan ALLAH da kuma Yesu Christi su shiga harkan hukuncin kisa ta yanda an karya doka ba. Domin dokan Yesu ne, kuma shi ne ya kuma gaya ma na abun da yake a yayen da ba’a kiyayeshi ba- wato gafara da alheri.
Wato yanzu, a laifin sata, ba ruwan gwamnatti a ciki- Wannan na nan sakanin mai abun ne da shi wanda ya yi satan, toh bayanannan Yesu kenan. Shi ba shi da jiki ko siffa. Ya kasance wai akwai gwamnatin kasa, ama shi gwamnati ne ma ma su bin sa. Su ba swa amfani da gwamnatin kasa. kuma a hakan ne ya na sanin mutanin sa, kuma ceto na kan faru ta hakan ne. Masu bin sa bai kamata su kasance da laifi ma juna ba ta wurin doka kauna, ama idan laifi ta kasance, hukuncin gafara da kuma alheri ne.
Muryan gwamnati ma na shine mu zo ga sammun ramako sa’alin da an mana laifi, ama kai mai bin yesu, ka san kana bin ALLAH bashin zunubi, wanda ya kuma ce ma na wai muna samu gafara idan mu gafarta ma wanda suna mana laifi ne (Luke 18:21-35, Mark 11:25-26), sanan wai zaka je kotu wai kana niman ramako?
Kuma ba wai na ce gwamnatin kasa bata da amfani ba. Idan ta kasance da soron ALLAH, toh. Ama idan gwamnatin kasan nan tana aiki da shawaran da ba nufin ALLAH ne ba, wato shawaran ramako, da kuma kin yancin kai na iya nuna gafara, kuma mun gan cewa dokokin ba swa fiskance abun da ALLAH ya ke so, toh, kun gan sai mu ja gefe daga wannan gwamnatin, ya cika wai gwamnatin ma su rashin bi ne.
Ama kuma, wani dalilin nuna kauna shi ne za mu gan cewa mutum abun rinjayi ne, wato dukan abubuwan da ya ke yi, daga zuciyan rinjayi ne ya yi su, wato akwai wani dalili ko gani da ya sa shi ya yi abun da ya yi, wato a zunubi, mutum yakan kasance da abun da ya rinjaye shi. A hakan za mu gan da cewa mutum ba kai ba ne a yayan da ya aikata zunubi. Shi ma ya aikata zunubin bisa ta zuciyan rinjayi ne. Dalilin da ALLAH ba ya hukunta mutum idan ya yi zunubi kenan, domin mutum ya kan aikata laifi ta wai ya rinjaya ne.
DAIDAI DA ALLAH.
Damuwan ba kama da ALLAH ba ne, damuwan zama abu daya da ALLAH ta wurin nuna hukunci ko hali dabam da wanda ALLAH ya ke. Kaman yanda na fada, ALLAH kauna da alheri ne, kuma ya kuma so dukan halitansa su zo ga zama kauna su ma. Kuma, sa’alin da shi mai gafara ne, a hakan kuma ya so dukan halitan sa su zo ga nuna gafara. Toh, ta wurin haka, muna iya cewa mu masu kamani da ALLAH ne, kokuma mu dai dai da ALLAH ne. Ya gamshe shi mu zo ga zama daidai da shi ta wurin dokokin sa, ta hakan mun gan da cewa shi kauna ne kuma shi ba ALLAH mai son kai ko yawan girma ba ne.
Dukan sujada ya tabata ga ALLAH ne, ama damuwan shine mu na dauki ALLAH da yawan girma ko kai da shi ya tambaya da kuma ya ke. Wannan kuma mun gan yana shafi yanda mu ke tunani da yin rayuwa ta yanda ALLAH ya yi niya. ALLAH bai halice mu domin mu yi ta bauta ma sa ba ne, ya halice mu alloli (ta kasan halitan mu) domin ya gan abun da ya ke, wato shi bisa kauna da alheri.
Ya kuma halice mu alloli ta wurin Yesu;
- Yanda mu na amfani da halin sa bisa na mu halin. Misali, kauna.
- Domin mu iya lura da kan mu. Ya halice mu alloli da na mu hanyoyin domin ta haka ne muna faranta ma shi zuciya, wato ta yanda kowa na da na sa baiwan dabam da sauran ama kuma baiwan sa mataimakon wani baiwa ne.
- Ta yanda mu na iya dauki yankin shawara.
- Kuma ina iya kara wai mu alloli ne ma ALLAH ta yanda ya halice mu dabam da shi domin ya gan kansa ta wurin abun halitan mu, wato kasan halitan mu. Muna faranta ma sa zuciya ta yanda mun kasance dabam da SHI, sai kuma muna iya tunani kaman SHI, har ga shaidan tunanin sa ta na mu hanyoyin.
Domin Litafi ma ya kira mu alloli (psalms 82:6). Ba za mu ki wai Almasihun mu ba Allah ba ne ama kuma sai mu alloli ne.
Duk wani tunani na ‘kadaici’ na ALLAH tunanni da kuma kokarin mu ne. Da gaskiya ALLAH daya ne, ama mu ma alloli ne ta wani yanayi. Shi kauna ne, kuma yanda takkadan farko ya gaya ma na, an halice mu ta kamanin sa ne. Ko wato domin shi kauna ne sai mu zama masu rashin kauna? Ko domin shi mai gafara ne sai mu zama ma su rashin gafara domin shi kadai ya kasance a halaye ma su kyau dinnan? Ama mun gan abin da ya ke ne shi ne ya ba mu a dokokin sa domin ya na so mu zo ga zama kamar sa. Domin ainayin dalilin halitan mutum shine domin mu fiskance ALLAH ta abun halitan mu ko kuma kasan halitan mu. Toh, za mu ki zama kama ALLAH domin mu na so ya kasance mai kyau shi kadai bayan da ya halice mu domin ya zo ga ganin kyau dinnan a ta wurin mu?
Ama abun da ke bata ma sa zuciya shine idan mutum ya zo ga zama dabam ta wurin nuna nasa tsarin doka da hukunci. Sa’alin da SHI kauna ne ma masu laifi, sai kuma a ce mutum kuma ya zo da nasa hukunci da ba kauna ba, kuma sai ya sake zuwa a cikin sunan ALLAH din kuma bayan da shi ALLAH ya yi magana ko a cikin Yesu Christi, wai kauna ne shi. Toh a hakan ne za mu ce mutum ya zama abu daya da ALLAH.
Yesu Christi da Ruhu mai tsarki da kuma mutum Alloli ne ta wurin kamani da ALLAH ta dokokin sa, ama sai kuma Yesu ne dokokin. Kuma a hakan ne mun gani da Maryamu da an so a jefe ta domin karuwanci (John 8:1-11). Ama sai Yesu ya kuma nuna abin da ALLAH ya ke ma masu laifi, wato kauna ta wurin gafara da alheri. Kuma a bayyan kauna din nan ne ta tuba. Toh, da a ce an kashe ta, da ta zo ga tuba ne? Ama da ta tuba, mun kuma gan cewa ALLAH ya yi nasara ta yanda ta zo ga tuba.
Ta wurin gafaran da Yesu ya ma ta, ya nuna ma na cewa;
- Dukan mu masu laifi ne, kuma a hakan, mutum bai kai na bayas da hukunci a madadin ALLAH ba. (Matthew 7:1-5)
- Sa’alin da mutum ya yi laifi, namu aikin shi ne mu zo ga kawosu su tuba ama ba yin mu su hukucin kisa ba, domin ba abin da ALLAH ya ke ba kenan.
Toh a hakan ne Yesu ya kuma kawas da dokokin kisa na yan israelawa. So bai kamata bayan haka a ce wai mutum ya zo ya tayar da dokokin nan a sunan ALLAH ba, domin dokokin ba su fiskance mutumin ALLAH ba, dalilin da shi kauna ne ma ma su laifi.
Tunani a wajen doka na nuna wai mun ki dokan, kokuma mun ba laifi ma dokan. Idan ALLAH kauna ne ta wurin gafara da alheri ma masu zunubi domin su zo ga tuba, bai kamata a ce mutum mai bin ALLAH ya zo ga ki da wannan dokan ALLAH’n ba. Idan ya (wato mutum) bayar da wani doka da ba kauna ba, shine zamu ce da shi ‘partner of GOD’ ko kuma ‘mai tsaye dai dai da ALLAH ta nasa shawaran doka’, domin ya nuna wai da ALLAH da kuma shi sun yadda cewa zunubin ba kyau, ama sun kasance da shawaran doka da ta bambanta. Toh a hakan, ba za mu ce Yesu ‘partner of GOD’, wato mai tsaye daidai da ALLAH ta nasa tsarin doka ba ne domin shi ya fiskance ALLAH bisa kauna. Kuma bai taba ce da wai ayi ma sa sujada ba, ama kuma shi ya koya mana cewa muyi sujada ga Uban mu, wato ALLAH. Duk abin da ma su bin Yesu sunna yi, nuna godiya ne ga yanda ya bar kujaran tsarkin sa ga ceton mu, kuma yanda na fada a takkadda na na farko, shi ne ya gama rayuwa ba zunubi ya kuma nuna mulkin ALLAH akan mutum yayan da mutum ya nuna cewa abun halitan sa ko kasan halitan sa ba zai iya shaidan rayuwan tsarki a cikake ba.
Duka zunubi zunubi ne ma ALLAH. Idan ya ce zai kuma yi mana hukunci, ai da ba mutum mai rai kuma. Toh, mu zo ga ki da hukuncin ma masu laifi idan mun karbi cewa mu yaran ALLAH ne. Domin ta wurin biyayya ga dokokin nan ne ALLAH ya na sanin mutanensa, kuma zai kuma ba su mulkin sama. Sa’alin da mu ma ALLAH na ba mu lokaci mu zo ga tuba, kadda mu kwace ma wayensu ma su zunubi na su lokacin tuba, da kuma na su shaidan kaunan da alherin ALLAH.
Ba yanda Yesu zai zama Almasihu idan ya cika Torah. Shi ya zo domin kiran masu zunubi ga tuba ne (Luke 5:31-32). Toh, ace wai Yesu kuma ya yadda da kashe masu zunubi, toh ai zuwansa a banza kenan, dalilin da wai shi ne nasaran ALLAH a kan zunubi bisa kalman ALLAH. Aikin sa ne ya kawo mutani ga tuba ta wurin kalmomin sa, yanda ya kuma yi. Toh mun gan bayyanda Yesu zai zo ga cika hukuncin Torah. Ai toh da ba shi da amfani kenan, wato idan zai zo ga cika abin da ke nan kamin shi, da bai kasance da suna Almasihu ko kalman gaskiya ba.
- Ama ta yayane kuna kiran ALLAH mai yafewa da kuma kauna bayyan da dokokin da kuna da shi da kun ce ya zo daga wurin ALLAH bai je dai dai da abin da kun ce ALLAH wa ma halitatun sa ba? Kun san ALLAH kauna ne kuma mai gafara ne ta yaya ne idan ba ku da shaidan nan ta dokokin ku? Ama mun gan da cewa da wai kun ce yesu ba daidai ne da ALLAH ba, ama shi ne ya zo ya fuskance ALLAH bisa kauna da kuma yafewa. Toh mun gan, shi a yanda ya nuna gafara da kuma kauna, shi ya na da kamanin ALLAH kuma ta wurin nuna kauna da yafewa, shi daidai ne da ALLAH. Kuma idan muma mun nuna yafewa, ana iya ce mu daidai ne da ALLAH, ama kuma ba mu ba ne ALLAH, domin duk kyau da muke din ya zo daga wurin ALLAH ne. Ama ta yayane kun ce ALLAH kauna ne ama kuma kun zabi horo da kuma hukuncin kisa? Kun gan sai mu ce mu ku da cewa ku ne ‘partners with GOD’ ko masu daidai da ALLAH ama dabam ta wurin dauka wani tsarin doka da ba kauna ba. Sai kun kuma kira masu bin yesu da sunnan laifin da ku ne kuna aikatawa.
- Yesu ne Kalmar ALLAH ko kuma Kalmar gaskiya. Sa’alin da mutum ya dauki wani shawaran doka da be je dai dai da mutumin ALLAH ba kuma ya ba ma mutani, to ya kuma yi karya a kan shi Yesu Christi, domin aikin sa ne (Yesu) sugabancin halitatu ta halin ALLAH, wato shi ne me bayas da dokoki bisa abun da ALLAH ya ke domin halita su aikata, domin shi ne sanin ALLAH ko kalman ALLAH. Dalilin da kuma ya na da ikon gafaran zunubi kenan (Matthew 9:6). Domin idan ka aikata ba daidai ba, ka fiskance shi ba daidai ba, toh kuma ka yi zunubi a kan sa kenan, domin ta wurin kalmomi da kuma dokoki ne mu na shaidan sa bisa kalman ALLAH. So idan ba mu yi shaidan nan daidai ba, toh ya zama mun gafarce sa, kuma yana bin mu bashin shaida.
ABOKANAYEN ALLAH.
Shi ne kalman ALLAH. Kuma a yanda aka ayana mun, shi ne yayi halita. Bisa kalman ALLAH, ya halice mu a kamanin ALLAH domin mu samu abokantaka da kuma sujada da ALLAH. Wato yanzu, shi ne hanyar sujadan mu da ALLAH kuma shi ne kuma sujadan mu da ALLAH domin sujada shine; tarayya da ALLAH. Muna tarayya da ALLAH ta wurin sa (Yesu) ne ta wurin dokokin sa domin shine sanin ALLAH bisa yanda ALLAH ya fitad da shi (haifuwan shi) ta wurin kalman sa, daidai da shi. Toh, duka dangantakan mu da ALLAH ta wurin sa ne. Ku ji ni; Yesu ne mahalicin mu, shi ne kuma sujadan mu.
CHANJIN KALMAN ZUWA JIKI KO MUTUM.
Toh a hakan ne shi ne maiceton mu, ta yanda ya yi shaidan mutumin sa (kalman ALLAH) ta mutuntaka ko ta jiki ko ta abun halitan mu, mana domin mu kuma yi tafiya ta hanyar gaskiya da kuma yi tafiya da ALLAH. Toh a hakan ne ya kuma sake halice mu abokanayen ALLAH ta kalmonin sa yayan da zunubi ya shigo har ga yanda mun yi dabam da ALLAH ta hali. A mutuntakan sa, shi dabam ne da mu, domin Ruhu ya halice sa kalman bangaskiya bisa abun da ya ke (Kalman ALLAH) da kuma bisa dalilin sa mana (Hanyar tarayya da ALLAH) domin mu samu tarayya da ALLAH, Toh ceton kenan.
Domin sa’alin da zunubi ya shiga duniya, sai mutum ya rasa hanyar tarayya da ALLAH, toh Yesu ne begen mu. Shi ne hanyar bangaskiyar da za mu kuma kasance da tarayya ta ALLAH. Kuma ceton nan sai ta wurin sa ne bisa kalman ALLAH, dole sai ya rege kai’n sa, daga tsarki zuwa bangaskiya domin mutum ya kasance da begen ceto, dalilin da rayuwan tsarkin da Ya so mu yi shaida ta farin halita ya rasu ta wurin zunubi. Shi ne begen mu da wai ALLAH bai rasa yadda na zuwan tuban mu ba. Shi ne ya kawo manar karfi da wai za mu iya kasance a tarayya da ALLAH a cikin zunubi. Ta yanda aka sa ma sa dukan zunubi domin ya dandana ya kuma yi nasara a kan su domin mu yi shaidan nasaran na a na mu ayukokin.
Daga farko da iyayen mu na farko sun yi zunubi, shi ya riga ya rege tsarkin sa yanda ya bar mutuntaka ta cigaba. Zaman shi mutum domin ya cika wannan regen kai da ya yi ko ne tun daga farko.
Ruhu tana kashe mu domin mu karbe sa (Yesu Christi), wato kalmomin sa. Ama shi, Ruhu ta na ba shi gaskiya ne ya gaya mana. Ta wurin Ruhu mai tsarki, shi (Yesu Christi) ya na shaidan kansa ne mana.
Ya bar tsarki ma bangaskiya, dalilin mutuntakan sa kenan. Don da an bi na rayuwan tsarki sa ne, da dukan mu mun mutu ko. Ama ALLAH ya turo shi ya kuma zama bangaskiya a cikin rayuwan laifi da zunubi domin ya komar da mu rayuwan tsarki. Misali; da an bi na sa ne, wato Yesu bisa mai tsarki, wato kamin ya zama mutum, da masu son kai sun mutu. Ama ALLAH ta wurin Kalman sa, wato Yesu, ya jumre da kashe su har ga chanzawan yesu zuwa kalman bangaskiya, don ta wurin Yesu bisa kauna, ma su son kai dinnan za su kuma zama ma su bayyaswa. Toh, nasaran ALLAH kenan a kan zunubi, domin da Yesu ya dinga kashe masu son kai bisa shi tsarki, toh, da bai fiskance ALLAH ba bisa mai jumrewa ba, kuma bai fiskance cewa mutum dinnan yana iya canzawa ba.
Ko mun taba ji wai wani ya yi ceto da kalmomin bakin sa ne inba shi ba? Manzanni duka yayan da sun kawo aikan dokoki da hali ma yayan Israela, sun yi shaidan sa ne. Sanan shi ne ya zo ya cika dokoki da halayen nan. Wato shi ne dokokin ALLAH kenan. Dalilin da muna shaidan sa kenan ta wurin Ruhu mai tsarki, domin shi ne ya cika rayuwan bangaskiya ba zunubi, ya kuma zama shi ne hanyan mu na ganin ALLAH.
Toh kuma dalilin da ya soko duniya kenan, domin yayan Israela ba su yi shaidan sa ba yanda ya kamata. Ba su fiskance sa yanda ya ke a gaban mutanin duniya ba, sai sun fisakance sa bisa hukuncin kisa da kuma nauyi ta wurin dokokin su. So ya kuma sauka ya bayyar da shaidan sa da kansa, domin ceton duniya.
Ama sai kuma yayan da Musulunci zata copa hali daga wurin Yesu, sai ita ta kuma copa daga yayan israela, wanda Yesu ya zo ya kawas da dokokin da kuma halayen su. Da Yesu ya zo ya cika Torah, toh da ba wani abu da wai ‘christianity’ ko ‘masu bin Yesu’. So ba yanda Yesu ya zo ya cika Torah, yanda Muhammad ya ambata a Musulunci.
Bazan giya ma ku, ta wurin Yesu Christi ne mun san da cewa ALLAH ba mutum ba ne, wato wanda yana jin haushi harga nuna fushin nan ta wurin hukuncin kisa. Mun gan cewa ALLAH ya ma fi kusa da masu zunubi ne, domin ya kawo su ga tuba. Domin ta wurin rayuwan hukuncin kisa, muna nuna cewa zunubi daidai ne da ALLAH kuma zunubi abun ban soro ne ma ALLAH. Ama ta wurin Yesu Christi, mun gan cewa ALLAH mai gafara ne kuma mai jumrewa ne ta yayen da mu kasance da zunubi. Ta wurin Yesu ne mun gane cewa muna cikin zunubi kuma kamata da mun mutu ne, ama Yesu ya kawo mana sanin zunubin nan bisa kalman ALLAH ko kuma kalman gaskiya domin mu zo ga tuba, toh a nan ne mun yi shedan alherin ALLAH.
Toh kamata Musulunci ta kuma yi biyayya ta wannan kalmomin yesu Christi ne, ama sai kuma bammu ganta tana yi ba. Dalilin da Yesu ya yi aika kenan wai a gaya mata wai ba da jumrewa ba za ya soko, su kuma yi hanzari ga kiyaye dokokin sa nan, domin kiyaye su ne ceto.
KOKARIN ALLAH GA HADA DUNIYAN TA ZAMA GUDA A CIKIN YESU CHRISTI.
Kokarin ALLAH ga hada duniya da kuma duka adinin su kasance guda daya ta wurin kalman gaskiya, wato Yesu Christi kenan. Kalmomin sa ke magana da ko wane mutum ne.
Bazan fara, Karbin Yesu alkawari ne sakanin mu da ALLAH, ta yanda mun karba cewa Yesu ne amsan dukan damuwowin duniyan nan. Kuma Yesu Christi ma na shine kokarin ALLAH a zamar da duniya guda daya a cikin Yesu Christi. Toh, ba wanda zai ce ya yadda da zaman ALLAH, sannan wai baya biyayya ga Yesu Christi. Kaman yanda ya fada mana; shi ne hanya kuma shi ne gaskiya kuma shine rai, ba mai iya kusa da ALLAH in ba wai ta wurin sa ba (John 14:6). Kin yesu ko kin kalmominn sa shine kin Zaman ALLAH ko kuma ba kuskuri wa ALLAH ta wurin Yesu Christi.
Sai kuma, tunda kun karbi cewa Yesu ne Kalman ALLAH, kuma Kalman gaskiya, dalilin me ne Muhammed ya halita nasa kalmomi da ya kawo ga Musulunci? Yayan da ALLAH na pama ya kawo zaman lafiya da kuma zaman tare a duniya, sai kuma Muhammed ya zo ya sa ga wani adini kuma, ya zo ya tayas da wani bambanci a kuma sunan ALLAH. Ya zo ya buga dan ragon nan ya kuma kafa nasa adini, bayyan da ALLAH ya kafa zaman sa a Yesu Christi.
A halitan Musulunci, Muhammed ya halita kishiyar Yesu ne chak chak. Duka abin da Yesu ya so ya kawas da shi a adinin Israelawa, shine Muhammed ya zo na taso da su kuma. Kun gani, bazan ma ku maganan gaskiya, Muhammed da Musulmai a yau sun kuma dauki ma kansu hali da sunan makiyin Kristi.
Shaidan Yesu wai Almasihu, shaidan mai zunubi ne ya bayar, bisa yanda Ruhu ta kashe sa ga ganin rayuwan Yesu da kuma kalman Yesu ne gaskiya.
Toh, me ne zunubi a Musulunci? Kuma me ne bayyanuwar Yesu a ta wurin zunubi?
Yesu ne sanin da cewa ALLAH ya gafarta mana zunubin mu (Matthew 9:5-6, Luke 7:48, John 8:7). Toh, ta yaya ne Musulunci ta cigaba da hukuncin kisa? Don meh ne Musulunci ba ta shaidan wannan gafaran da Allah ya ba ma masu laifi domin su zo ga tuba?
GWADIN ALLAH KO ABUN (HALICIN) ALLAH TA ABUN HALICIN MU TA WURIN AYUKOKIN MU/ DAN TUNKIYA BISA MAI RASHIN LAIFI DA KUMA RASHIN ALHAKIN LAIFI.
Gwadin ALLAH ta abun halitan mu ko kasan halicin mu; wato mutum zai dinga nima da kuma halita “daidai” da “ba daidai ba” a ayukokin sa. Toh kuma abun da ya (ke) kawo ga nauyin ko wahala a adini kenan.
- Ta yaya ne yesu mai ceto ko Almasihun ku? Eh, kwarai, kamata mutum ya kasance da niman “daidai” da “ba daidai ba”a ayukokin sa domin niman daukaka ko niman tafiya da ALLAH. Ama wannan yakan zama ma mutum da nauyi sosai kaman yanda mun gani da yayan israela (Misalin wani halin shi ne a Matthew 15). Kuma halin ma, ba bukatan ALLAH ba ne gare mu. Akwai ayukokin da zamu nima daidai da kuma ba daidai ba domin mu yi sujada da ALLAH, ama ba ta wurin abubuwa kankani ba. Akwai abubuwan da duk ma kan mu ne ba ma ALLAH ba, wato akwai abubuwan da suna fiskance mu alloli, wato mutani masu ayukokin su. Toh Yesu Christi mana kenan, shi ne ya kawo mana sanin ALLAH dinan, da wai ALLAH bai tambaya niman daidai da ba daidai ba a komin da za mu aikata.
Toh bai kamata Musulunci ko Muhammed ta kuma sake halita wanan halin a kan mutani ba, tunda ta tabatta wai Yesu ne kalman gaskiya ko kuma kalman ALLAH, dalilin da Yesu Ya zo ya kawas da halin nan (Matthew 15:20) bisa wai nufin ALLAH ne ma mutum, a yanda masu lura da dokokin israela sun kafa a kan mutani.
Yan Israela na da, sun shiga halin gwada ALLAH, ko kuma halin ‘halici ALLAH’ ko halin niman daidai da kuma ba daidai ba a ayukokin su. Sai kuma sun zo ga zama da adinin abu mai nauyi akan mutani. Misali yanda suka kafa dokan wanke hannu kamin mutum ya ci gurasa (Matthew 15), ko kuma wanke tukunya ciki da waje kamin a yi amfani da shi. Toh ba su sa dokokin nan a wai halaye masu kyau ba, sun sa su bisa wai dokokin ALLAH ne, wato halin ALLAH ne, kuma idan mutum bai yi haka ba, toh ya karya dokan ALLAH, wato zai je wuta.
Ama ALLAH mutum ne?
Toh zuwan Yesu bisa mai ceton su kenan, domin shi ne kalman ALLAH ko halin ALLAH sanan ya kuma gaya musu kalman gaskiya da cewa, ALLAH ba nauyin kaya ba ne a kan mutani, ama dai sai mu yi rayuwa Kaman yaran da ba su san komi ba, ko yanda na yi shaida ta Ruhu mai Tsarki, Yan tunkiya da basu san komai ba.
Toh halin da Muhammed ya zo ya kuma tayas kenan; halin gwada ALLAH bisa ayukokin sa, halin niman da kuma halin halita daidai da ba daidai ba a ayukokin sa. Sai kuma ya kuma sa wanan halayen wai dokokin ALLAH ne a kan mutane.
Misali; shigan dakin bayan gida da kaffa na hagu, kuma amfani da dusuna uku ma share jiki. Ga kuma yanda za wanke jiki; farawa daga dama zuwa hagu, da kuma son nawa mutum zai wanke ko wane sashi na jiki. Ga kuma yanda mutum zai zauna ko durkusa a adu’a. Ga kuma yanda mutum zai shiga masalaci da kaffan dama sai ya fita da kaffan hagu. Ga kuma yanda mutum zai yi adua a shigan gidan bayan gari da fitawa, ko zai bar gida, da wurare dayawa. Ga kuma cin abinci da hanun dama, ama sai mutanin da ALLAH ya halice da hanun hagu fa?
Kuma duk wayanan halayen halita daidai da ba daidai ba ma zuciyan mutum ne, wato ma koshiyar da hankalin mutum, da wai ya yi ‘gaskiya’.
Ni na gane da wannan halin domin dah ni ma na kasance da irin wanan halin. Kuwa Yesu ne ya cece ni. Kuma har yau ina dan pama in bar wayesu halayen domin sun zaman mun kaya masu nauyi. Toh dalilin da ALLAH ya yi domin in yi magana da ku kenan ku zo ga gane yanda wannan halin ko adini yakan fara har ga yanda ya bayanna.
Zunubi duk abin da ba ALLAH ba ne. Toh sa’alin da mutum bai fiskance ALLAH ga yanda ya ke ba-ta wurin kalman sa ba, toh, zunubi kenan. Kuma sa’alin da ALLAH hutu ne ma halitan sa, toh zan kuma gaya m aku da wai halin niman daidai da ba daidai ba a ayukokin mu zunubi ne. Kuma ta yanda kun kuma kafa shi wai adini, toh wanan babban zunubi ne. Mu masu bin ALLAH, muna fiskance sa ne ta wurin dokokin sa, kuma idan ba mu fiskance sa daidai ba, mu kan zama da shi da wiya ma wanda ba su san ALLAH ba su zo ga karbin shi. Dalilin da ya kamata mu na lura da irin abubuwan da muna kira wai dokokin ALLAH ne.
Abun halitan mu, wato kasan halitan mu ba abun gaskiya ba ne har ga wai gwadin (mutumin) ALLAH ta ayukokin mu. Domin idan ku ce wai Musulunci shine adinin gaskiya, toh kun gaya mana cewa kun kuma halice abun ALLAH ta jiki. Kun kuma gaya mana cewa kun gwada ALLAH ta jiki. Kun kuma ce wai kun halice tsarkin ALLAH ta ayukokin ku. Ama kwarai, ba ku yi ba. Kuma mutum bazai taba iya ba. Duka irin wannan dokokin da hanyoyin tunanin mutum ne bisa abun da sujada wa ALLAH ya ke. Mutum bai san ALLAH ba da wai zai shiga halitan daidai da ba daidai ba a ayukokin sa, toh Yesu Christi mana kenan.
Domin an gaya mana a hadith yanda Muhammed ya tsaya yayi adu’a har ga kunburin kafufuwan sa, ko kuma yanda Zainab ta rike igiyoyi biyu bayan ta gaji da adu’a a tsayen kanta domin ta cigaba da adu’a.
An kuma gaya mana yanda Muhammed yakan sa mutani su dinga ta fada kalamai guda daya ta wurin yin adu’a ko daukaka ALLAH. Duk wanan halayen da kuma tunani, su ne Yesu ya zo ya kawas da su (Matthew 6:7).
Mutum bazai taba iya daukaka ALLAH ta iyawan sa ko karfin sa ba. Sujadan mu kowai shi ne kiyaye kuma biyayya ga dokokin ALLAH. Kuma sujadan nan ne Yesu ya ma na ta wurin halita ma na dokoki domin shi sanin ALLAH ne, toh a hakan ne shi kalman ALLAH ko kalman gaskiya. Domin da ba ta haka (shi, wato Yesu) ba, da ba za mu iya tafiya da ALLAH ba, ko tarayya da ALLAH. Kuma bazai iya faru da wai mai zunubi ne ya kuma halita dokokin ceton sa ba.
ALLAH kuma bai bukata irin wannan sujadan daga wurin mu ba. Bai tambaya ma wanan ba, shi ya tambaya mu kiyaye dokokin sa ne kowai. Duka wani irin sujada halitan mutum ne. Ama ALLAH bai hana mu yin wani irin sujada ma sa ba, ama idan za mu doki sujadan nan da muhimmanci fiye da kiyaye dokokin sa, toh, a wurin Yakan samu damuwa da mu. Kuma duk sujadan da za mu yi mishi, kadda mu karye dokokin sa ta wurin aikata wanan sujadan. Na karshe, kada sujadan nan ya kasance mana da nauyi, domin shi ba nauyi ko wahala ba ne a kan mu. Idan mun zabi adini mai nauyi kuma mun sa a kan mutani wai dokokin ALLAH ne kuma hanyar ceto ne, toh munyi karya a kan ALLAH, kuma zunubi ne.
Toh a hakan ne Yesu mai ceton mu; domin shi ne ya zo ya cece mutanin israela daga nauyin adinin da masu lura da dokokin gari suka sa a kan mutani bisa wai hanyar ALLAH ne.
Toh a hakan ne ya cece muma da ba yayan Israela ba; Don da ya zo ya kiyaye wayanan nauyin dokokin, toh, da mu ma muna cikin wannan adini mai nauyin da wai gaskiya ne, domin niyan ALLAH shi ne ya yi amfani da yayan Israela ne ga ceton duniya. Kuma ta wurin kiyaye kalmomin sa, da ta wurin yadda da cewa ya soko daga wurin ALLAH da sakon ceto mana (John 17:24-26), shi ne mun karbi kalmominn sa nan bisa gaskiya da kuma nufin ALLAH ma na.
Toh kuma ceto ma na kenan, wato karbin wai Yesu ya zo daga wurin ALLAH, inba haka ba, da duk biyayya wa kalmomin sa a banza ne idan mutum da mu na biyayya ma kalmomin sa bai san ALLAH’N da ya na mana Magana a kai’n sa ba. Ko ku kun gan da cewa ba laifi wai mutum da bai san ALLAH ba ne zai sugabance mu ma ALLAH?
So ba yanda za’a ce wai Yesu ya zo ya cika Torah, misali; hukuncin kisa da rayuwan niman daidai da ba daidai ba a ayukokin mu. Domin shi ya zo ya daina zunubi ne ta wurin kauna, da kuma shi ya kawo mana hutu ta wurin zama Kaman yara ko yan tunkiya. Domin idan ka kaunace ni, ba za ka yi mun sata ba, ko ka kwache ma ni mata, ko kayi karya a kai na ba. Kuma idan mu kaunace ALLAH, ba za mu bauta ma komi; ko dutse ko mutum ko gunki ba, domin shi ba abubuwan nan ba ne. Shi kalman sa ne, kuma kiyaye kalmomin nan ne shi ne sujadan mu, toh, Yesu Christi mana kenan. Ama kuma israelawa na dah sun yi hukunci ne idan an kayre doka. Ama hukunci ba ta daina zunubi ba, kauna ne ainayin dokan da na kawas da zunubi.
Gaskiyan shi ne, ALLAH ya na iya zama yanda Yayan Israela ko Musulmi sun sa shi, wato ALLAH’N hukuncin kisa. Kuma kauna da mun gani ba yancin dole ba ne, alheri ne. Ma su bin Yesu su na raye ta alherin ALLAH ne ama ba yancin dole ba ne wai a gafarce su, ko a ba su ikon gafara.
RASHIN LAIFI/ RASHIN ALHAKIN LAIFI.
Ya tabatar ya share kanshi. Idan wani ya samu rima a kayansa, bayan haka, sai ya koshiyar da kansa da cewa, “wannan ruwa ne kowai”. Wanna bisa hadith ne wanda Al-Hakin ibn Sufyan ko Sufyan ibn al-Hakim ya ce, “Idan manzon ALLAH, salama ya kasance a kan sa, ya yi pisari, sai ya wanke da kuma yayyafa ruwa akan abun pisarin sa”. A yanda wani ya fada kuma na ce, “Na gan manzon ALLAH ya yi pisari, bayyan haka sai ya yayyafa ruwa akan abun pisarin sa”. Ibn ‘Umar ya saba dinga yayyafa ruwa akan abun pisarin sa, har san da tufafin sa ta jiku.
Wannan ne muke ce da shi alhakin laifi daga rashin sani. Abun da yakan kawo ga irin wayannan halayen, sa’alin da mutum ba shi da sani akan abubuwan da ya na yi- ko ya je daidai da nufin ALLAH, ko bai je daidai da nufin ALLAH ba.
TABBACIN ALLANTAKAN MU.
Mu alloli ne ta abun halitan mu, wato kasan halitan mu. Mun kasance da hanyoyin mu -wanda kuma ALLAH ya ke amince da su. Domin ta haka ne muna iya faranta zuciyan ALLAH, sa’alin da ya gan mutani masu zabi da kuma iko suke yanke shawara. Ama dai yanken shawaran nan su na faranta zuciyan ALLAH idan mun dauke su a cikin halin ALLAH, wato kauna, da hutu, da rayuwan tsarki, da rayuwa kaman yan tunkiya ko yaran da ba su san komi ba.
Rayuwa ta zuciyan yaro ko dan tunkiya ne ke ba mu yanci a na mu ayukoki, ta zuciyan nan ne mu na samu yanci mu aikata ayukokin da halaye, kuma zuciyan da babu alhakin laifi din nan ne ke ba mu tarayya da ALLAH, wato rayuwa ta zuciyan yan tunkiya ne ke nuna mu ‘ba laifi a gaban ALLAH’. Rayuwa Kaman dan tunkiya ko yaro wanda ba shi da alhakin laifi ke bukata sanin ALLAH domin kadda mutum ya zo ga rayuwa da zai karye dokan nan, Toh Yesu Christi mana kenan. Sa’alin da shi ne sanin ALLAH ko kalman ALLAH, a wurin kiyaye dokokin sa ne za mu san ba mu da laifi, ama sa’alin da ba mwa kiyaye dokokin nan, toh mu na da laifi ta wurin yin rayuwa ‘a wajen ALLAH’.
Abun da ya kuma kawo ga adinin halita abun ALLAH daga na mu abun halita shine domin mutum ya kasance ba shi da ‘yadda da kai’ ko kwarin hali a ayukokin shi. Toh wannan ya nuna rashin sanin kalman ALLAH ne bai ba mu yanci ma namu ayukoki ba. Toh yayan da mu alloli ne, wato mu na da yanci a wayansu ayukokin mu, ama adinin nauyin nan ya kawo ma mutum ga kin karbi allantakan sa ta wurin nima ya yi ma ALLAH ‘sujada’ a komai’n da zai yi.
Akwai abubuwan da muke yi, da ba ma ALLAH ba, ama ma kan mu ne. Misali wai wuni zai koya miki yanda ake tafiya bisa ga adini, ko yanda ana zama ga adini, wannan duk ma kan mu ne. Ama kuma akwai irin halaye da na duniya ne, misali, irin tafiya wai takawan muskule, ko Magana ta wai ‘fuck’ ko ‘damn’. Mun gan da cewa irin kalmomin nan ba kalmomin da suke nuna mu yaran ALLAH ba ne, domin kalmomin nan daga niya ne wanda ba kyau, kokuma ba swa zama a kan zuciyan ALLAH na rayuwan yan tunkiya.
Da gaskiye, nima ga girmama ALLAH ne (ama) ya kawo irin wanan halin da adini, ama ALLAH ba gunki ba ne, wato, za mu ji sa ne a yanda zamu girmama shi ama ba wai zamu halita ma sa na mu hanyoyin ba ne. Kuma hanyoyin sa ne ya ba mu ta wurin kalman sa, Yesu Christi.
YARON ALLAH TA BIYAYYA GA ALLAH DA KUMA TA ZUCIYAN WANDA BA ALHAKIN LAIFI.
Sa’alin da Yesu ya kira kansa yaron ALLAH, eh, kwarai shi be yaron ALLAH ta yanda muna tunani ana samun yaro ba. Ama ya kira kansa yaron ALLAH da zuciyan mutum da ba shi da laifi ko rashin alhakin laifintunanin mu na Yaro bisa ta wurin Jima’i. Laifi na kasance, ama ba kai’n da za ba sa laifi dinan. Ko kuma, kai din bai kai na dagan laifin ba.
Ama abun da ya kawo har ga Yesu ya kira kansa yaron ALLAH a sakanin su farisiyawa shi ne domin dokokin da su na kafawa ba dokokin ALLAH ba ne. Toh, shi ya raba kansa bisa yanda shi biyayyan sa ga ALLAH ne, ba ma farisiyawan ba. Dalilin da har ya koyas wa da yayan israela wai Ubansu ALLAH ne (Matthew 6:9, 5:16 & 48 18:4, 23:9. Luke 11:13, Mark 11:25), domin koyaswan su farisiyawan ba daidai ba ne, kuma ta yin haka, ya sa kansa ne hanyar ceto da kuma hanyar tarayya da ALLAH. Yesu ne kalman ALLAH, ama kuma sai su na ba ma yan israela kalmominn da ba shi ba ne, wato kalmomin da ba daidai ba. Toh, ya na kuma koya wa yan Israela da cewa shi ne hanya ga ALLAH, wato, ta wurin sa ne mutum ya na kasance yaron ALLAH ta wurin kiyaye dokokin sa.
Asalin Yesu ba mutum ba ne. Ya kasance mutum domin ceton mutum ne. Girman sa ya fi mutuntaka. Idan ya kasance kalman ALLAH, ma na ne mu yi amfani da shi a rayukan mu.
HAIFUWAN MUSULUNCI.
Ama kun gan Musulunci ta zama adini mai rayuwa ta alhakin laifi. Nasaran ALLAH shi ne ma na mu zo ga rayuwa kamar wanda ba su san laifi ba. Domin idan mun kasance a zama adini daga laifofin mutani, to wato muna bukatan zunubi kenan domin mu dinga zama ma su gaskiya? Wato ALLAH na bukatan laifi kenan kamin a waye sa? Duk adini da ta kasance adini mai alhakin laifi, toh, kun gan ba ta da yanci.
Misali, sa’alin da Farisiyawa sun yi niyan kashe Yesu da wai ya ce shi Yaron ALLAH ne (John 10:30-36), da shi ya na iya ce, “toh me ne a wurin, bazan yi shiru da maganan nan kowai domin in samu zamn lafiya da su (farisiyawa), kuma domin in yi rai.” Ai kwarai ya san dokokin su, ya san da cewa tsarin doka ma sabo mutuwa ne. Ama shi bisa dan tunkiya, bai bar tunnanin su farisiyawa din ya kasance a kan sa ba, in ba haka ba, da zai kasance da alhakin laifi konda shi ba shi da laifin, wato irin tunanin su. Toh, ta shi ne ko ta zuciyan sa ne ko ta dokokin sa ne mu ma mu na da yancin kiran ALLAH Uban mu.
Sanan mun gan da cewa har an kashe shi domin ya cigaba a rayuwan rashin alhakin laifin sa, da wai shi yaron ALLAH ne.
Abun Kaman ka na angwan da ana sata ne. Toh sa’alin da kowa yakan rufe kofar dakin shi da kwado domin kadda a shiga a yi sata, ama sai kuma Yesu ya ki rufe kofan dakin shi, har ga yanda aka shiga an sace komi. Shi bai yadda da zaman sata ba. Bai bar halin da ba kyau din nan ya dauki salaman sa ba. Toh mun gan a bayan haka ne ya cika zaman Yaron ALLAH, domin shi bai kasance da alhakin laifin satan ba. Toh rayuwan da ALLAH ya na so mu zo ga yi kenan. Rayuwa ta rashin laifi da alhakin laifi.
Mumunar rayuwar zama da alhakin laifi shi ne, konda mutum ba mai sata ba ne, rashin zama ba yanci daga alhakin laifi na iya sa mu mu gan kowa ma kaman barawo ne, kuma idan ka dauki mutum da ba mai sata ba da ganin shi barawo ne domin wai ana sata a angwan, toh ka ma sa laifi. Ama bayannuwar Yesu Christi ma na kenan, wato ma su bin sa su kasance da yanci da kuma aminci sakanin su.
Yancin nan (da Yesu ya kasance a ciki) doka ne ma masu bin ALLAH domin abun da ALLAH ya ke kenan, kuma Yesu ya zo ya cika wanan halin. Toh sai kuwa ya zama ma masu bin ALLAH doka ta hali, wato duka kasancewan mu ya zama munyi a yanci. Dalilin da ya kamata mu zama masu rashin alhakin laifi kenan, domin ALLAH yanci ne.
Nasaran ALLAH shine rayuwa kamar yan tunkiya domin mu zo ga nasara a kan zunibin nan, kuma mu fiskance nasaran ALLAH a wurin da zunubi ko laifi ko alhakin laifi ta kasance.
Musulunci ta kasance adinin daidai daga alhakin laifi, ama ba adinin yanci daga rashin alhakin laifi ba. Ita ba ta nuna nasaran ALLAH a fiskan laifi da kuma alhakin laifi ba.
Toh mun gan Yesu Christi ne ya zo ya nuna nasaran ALLAH, a yanda ya kira kansa yaron ALLAH, kuma ya kuma kira mu yaran ALLAH, ama ba ta wurin jinni ko jimayi ba. Yaro ta wurin jinni ko jimayi shi ne tunani da kuma hanyan mutum ama ba na ALLAH ba. Kuma a hakan, akwai gaskiya a yanda mu yaran ALLAH ne; domin ko iyayen mu ma ba su waye mu kamin sun haife mu ba. Su ma sun same mu a yanda mu ke ne. Abun da mu ke ya kasence da ALLAH ne kowai.
Sai kuma Musulunci ta zama adinin da ta kasance da nauyin yin yaki da zunubi. Misali; ba laifi ba ne miji da mace su rike hannu su yi tafiya. Ama a yau, domin iskancin mutanen turai, sai kuma a sa doka wai kadda mace da miji su rike hannun su. Ama kuma su, ba su da laifi zunubin isakancin nan. Ko kuma, sa’alin da na maza su na iya rungume junan su, ama domin maganan luwadi, sai a sa doka wai kadda maza biyu suyi kusa da junan su, ama kuma ba su da laifin luwadin nan.
Abin kamar mun ji cewa shaitan dan hannun hagu ne. Sannan mun sa doka wai kadda kowa ya yi amfani da hannun hagun sa domin hannun da shaitan ke amfani da shi kenan. Ama se ga Yesu Christi ma na; Sa’alin da ban da zunubin shaitan dinnan, toh be kamata in dauke alhakin laifin sa ba. Ta wurin rayuwa kamar dan tunkiya, zan yi amfani da hannun hagun nan har ga chin abinci.
Mun zama kamar mutum mai tsaye a mike, ama garin tura mumunar abun wanda ke gefen sa, sai kuma ya lonkoshe, toh mun gan ya kuma rasa tsaye a miken sa. Toh Yesu Christi ne ya kawo ma na hanyan da za mu kasance a tsayen nan ba da kula da mumunar abun da ‘na gefen mu’ dinnan ba- ta wurin rayuwa kamar dan tunkiya. Toh a haka ne ya kuma kawas da zunubi ko kuma alhakin zunubi, da kuma alhakin gwada mutumin ALLAH a ayukokin mu.
Misali kuma; “ba allah in ba ALLAH ba”, da kuma “ALLAH ba shi da daidai” Toh maganan nan ta fito lokacin da akwai masu bauta ma su gunki da wata kila ma masu bin Yesu domin mun ce Yesu ma Allah ne. Toh yanzun da ba masu bauta ma su gunkin nan a kasacen musulmi, ama sai ya kun kuma kasance a kalmomin “dai dai” dinnan? Toh, kuma ba wai ma su bin Yesu sun ce Yesu shi ne ALLAH ba, ama litafi ma ya kira mu Alloli (psalm 82:6, John 10:34-36). Kuma yanda na bayana, ‘allah’ bisa kalma, ke iya nufi abubuwa dabam dabam.
Kuma a yanzun da ba masu bauta ma gunki, kun dauki nauyin alhakin laifin masu bauta ma su gunki ne. Kalman da wai “ba wani allah in ba ALLAH ba” da kuma “ALLAH bashi da daidai”, bisa rayuwan ka da kuma adu’an ka ma ALLAH ne ke nuna cewa kai kana bauta masa SHI kadai ne.
Laifin rayuwa ta dokokin alhakin laifi shi ne ya na zaman da kai wanda ba shi da laifi din, mai laifin. Ya na sa maka zunubin laifi din, kuma sai ya dauki yancin ko sakewan ka, bayan da kai ba ka da laifi din.
Toh, wanan’ne ana ce da su bangaskiyan kai ko gani. Wato mutum ne yana ba ma ALLAH ta na sa tunanin, bisa ganin sa abun da ALLAH yake. Musulunci tana fisakance ALLAH mutum ne ta bauntan sujadan su, bisa wai hanyan gaskiyan bauta wa ALLAH kenan. Eh, yana da kyau mutum ya zo gaban ALLAH da nuna girma ma sa. Ama wannan ba abun da ALLAH ya tambaya a kan mutum ba kenan. ALLAH ke ganin cikin zuciya ne idan mu na ma sa sujada. Wato, ko kana tsaye ne, ko a zama, ko a kwance, ko ka durkusa, ALLAH na iya ba kunyen sa ma sujadan ka. Ama idan ka zo gaban sa ko a kwancen kasa, ama zuciyan ka bai kasance da tunanin sa kadai ba, toh duk wannan bautan a banza ne. Kaman yanda Yesu ya gaya ma matan da ke diba ruwa a rijiyan nan (John 4:24). Adu’a ta wurin zuciya ne ta cikin gaskiya da Ruhu, domin ALLAH Ruhu ne ba mutum ba-wanda zai damu da irin bautan mu. Misali; Kaman yanda mu na bauta ma su sugaban mu, da su sarakunan mu, da su kakanin mu, da su iyayen mu, toh, ka gan su, ko zuciyan ka na nan a bace ama dai ka durkusa ko bauta masu, sukan yi farin ciki, ama idan ka zo gaban ALLAH ko a kwancen kasa ama zuciyan ka ke nan da rashin yanci ko wani mumunan abu a ciki, dukan wanan bautan a banza ne. SHI ALLAH ne, kuma ya fi kasan (abun) haifuwan mu gabaki daya-wanda wai zai ji mu bisa yanda mun bauta masa ne.
Domin a haka, Musulunci ta zama kamar adini na kai da kuma na mutum, ta wurin da mutum ne ya na sasanta ma kansa da cewa ALLAH daya ne kowai, kuma ba shi da daidai, da kuma yanda mutum zaiyi sujada wa ALLAH. Domin tun daga farko, ALLAH bai kasence da wani Allah ba, so bai kamata mu na zuwan gabansa mu na gaya ma sa da cewa ba shi da na biyu, kuma tun daga farko, ya kasance da halin sa wanda ya kamata mu yi biyayya ga su ne kowai, ama ba wai mu ne za mu halita hanyoyin sujada wa ALLAH ba.
Toh, kamar yaro jinjiri ne, akwai wanda zai ma sa bulala idan ya yi pisari a jiki? Ya na da sanin wani abu ko ne? ko kamar ita yaron jinjiri din, akwai mai iya ma sa bulala wai ya na yawo a sirara ne? Yana da sanin jimayi ne? Toh a haka ALLAH ya na so mu zo ga rayuwa- ta rashin sanin duk abu mai zunubi.
Misali, doka ya ce wai yaro ya bar baba ya wuce kofan kamin shi, ko kuwa, idan yaro ya gan tsoho, sanan sai ya tashi ma tsohon nan ya zauna. Wanan doka ne, kuma dokan nan Yesu ne ya kafa, ama dokan nan kuma ba Yesu ba ne. Yesu kauna ne, kuma ba shi da jiki ko siffa, wato, ta zuciyan Yesu bisa gaskiya, baba ya na iya barin yaron nan ya wuce wanan kofan kamin shi, kuma tsohon nan na iya tashi ma yaro ya zauna, domin kauna ba shi da siffa ko bangare. Yesu ya kaffa dokokin bisa irin mutanin da ya ke jagorance ne, irin mutanin ma su son girma da kuma son kai ne, kuma mutanin doka ne. Ama ta wurin Yesu, wato mutumin sa, ba wani abu wai doka ama kuma dokan kauna ne.
Misali kuma, Yesu ya amince da rayuwan baptisma, ama kuma ba baptisma ba ne na nuna mu yayan ALLAH ko masu bin Yesu, dokokin ALLAH wanda Yesu ne ya kawo ke nuna mu masu bi da kuma yadda da ALLAH ta wurin Yesu (John 13:34-35). Kokuma yanda wai jini ne na wanke zunubi, ama kuma kalman ALLAH ne ke wanke zunubi kuma ga kawas da zunubi (John 15:3), domin jini bai kawo ma na sanin zunubi ba, ama kalmomin Yesu ne sun kawo ma na zunubi, domin mu daina su.
Abun da ina so ku zo ga sani shi ne; akwai gaskiya, kuma akwai daidai. Misali, sa kaya ga rufen duka jiki daidai ne kuma doka ne ma yayan ALLAH domin kasancewan zunubin jima’i, ama kuma kasancewa a cikin cikeken kaya ba gaskiya ba ne, domin rayuwa ta rashin kaya ne, wato rayuwa ba sanin jima’i shi ne ALLAH ya nufa ma na ta farko (Genesis 2:25).
ALWALA.
Misali, zancen alwala bayyan pisari ko wani kazamta ya taba jiki; eh, sapta na da kyau, ama saptan nan ma na ne ba ma ALLAH ba. Eh, da gaskiya datti bai fiskance ALLAH ba, ama kamata muje mu saptace wurin ne. Yakan faru cewa ba da niyan mutum ba ne kazamta ya kasance a jikin sa, toh abun yi shi ne mutum din ya nima na wankewa domin shi ma ya samu sakewa da yanci. Ama idan babu abun wanke wannan kazamtan, toh, tun da ba wai ya yi wannan kazamtan da sannin shi ba, ALLAH baya dauki nauyin zuciya domin wannan. Ama idan akwai abun wanke kazamta din, sai mutum din ya je ya share wurin da ya kazamtatu din, ama ba wai sai ya je ya yi alwala wai domin yana niman tsarki ba. Ruhun ALLAH ta wurin kalman ALLAH (sapta) ne kowai ke ba ma mutum zama a tsarki idan mun kiyaye dokokin ALLAH, ama ba ruwa ko alwala ba. Kuma sai mu tambaya, tunda kun dauki pisari kazamta har ga bukatan alwala da tsarki, sai zufa fa? Don me ne ba’a alwala ma zufa?
NAUYIN ‘SUJADA’ NA ADINI.
Domin Muhammed a hadith ya ce; idan ba don wahala a kan mutani ba, da zan sa su su dinga wanke baki da magogin hakora ma kowane alwala. Kuma ya sake cewa; da ba don wahala a kan mutani na ba, da na sa su su dinga yin alwala ma ko wane adu’a. Toh a nan, mun gan cewa Musulunci halitan Muhammed ne bisa na sa sujadan ma ALLAH. Ama kuma mun gan da cewa a halita hanyoyin sujada din nan, ya na gwada ko halita mutumin ALLAH ta ayukokin sa ne.
Toh ba zan gaya mana wani abu; idan maganar adini ne, zan ce ma Musulunci ba ta fara adinin ko ba, da za ce wai kun kasance adinin gaskiya. Idan kun bi na gwada ALLAH ko kasancewar ALLAH ta ayukokin mutum yanda Isaraelawa na da sun yi, ku da kanku za ku nima barin harkan ALLAH, domin ba karamin nauyi da wahala ba ne da hidiman. Ama Yesu mana shi ne, sai ta rayuwa kamar yaro karami ko dan tunkiya shi ne za mu sa mu yanci daga bautan gwada kasancewan ALLAH ta ayukokin mu, da wai sujada ne.
ALLAH cikake ne. Ba mua iya kara ma sa komi ko mu rage ma sa wani abu, sai dai ko shi ya dinga ba mu ko ya dinga rage ma na. Toh, Yesu ma na shi ne; ALLAH ba ya damu da na mu hanyoyin ma sa sujada domin ba ya kara mi shi komai. Idan zamu yi, mu san mu na yi ma kan mu ne, mu san mu na shaidan girman ALLAH ma kan mu ne. kuma kadda mu sa shi doka a kan wani, mu kuma tabatar cewa ba doka ko halin nauyi ba ne a kan mu. Duk abin da ALLAH ya ke so, da ke faranta ma sa zuciya shi ne mu bi dokokin sa, domin mu sa mu tarayya da shi.
Toh a nan ne Yesu ya kawas da adinin na Israelawa domin dokokin su bai fiskance mutumin ALLAH ba.
YESU BISA MISALI MANA.
Kuma wanan ne begen mu, zuwan Yesu domin ya zama ma na misali, domin da ya yi ma na aikin mu, wato kiyaye dokokin ALLAH, toh, da ba za mu kasance da amfani ma ALLAH ba, kuma da la’anta na mu kenan-ta yanda wai ba za mu taba iya kiyaye dokokin ALLAH ba. Domin Yesu ya zama mutum kuma doka mana, ba don ya la’anta na mu bane, ama ta wurin konlon shi, muma sai mu zama Kaman shi. Bai (Yesu) doki allantakan mu ta wurin doka ba, ko ta wurin zaman mutum na shi ba, ama ta wurin bayad’da doka, za mu yi koyi mu kuma aikata dokokin nan ga ceton mu. Toh, Yesu bisa maiceton mu kuma kenan, ta wurin kansa, wato rayuwan sa da kuma ta dokokin da ya furta ma na mu kiyaye. Dokokin nan halin shi ne da ya ba mu mu zama bisa masu bin sa ko ma su bin gaskiya.
“ALLAH bai dauki wani yaro ba, kuma ba wani Allah da ya taba kasance da shi. Da akwai, da kowane allah din zai dauki abun da ya halita, sai kuma wayensun su, za su nima su rinjayi sauran. Daukaka SHI akan kwatance da sun yi a kan sa”. (QS. Al-Muminoon 23 verse 91).
- Ama me ya kawo ga tunanin da wai ‘allolin’ za su samu damuwa sakanin su? Mun gan alhakin laifin rayuwan Muhammed, mun kuma gan irin tunanin sa. Wai ya gaya ma sa da wai allolin za su rinjaye juna? Konda akwai alloli uku, lai lai ne su yi fada?
Toh a nan mun kuma fahinta tunanin Muhammed. Ya dauki alloli uku din ya zama mutani dabam guda uku ne. Ya dauki kalman ya zama mutani masu girma dai dai.
ALLOLI UKU/ HUDU (wato da mutum).
Sa’alin da mun ce ALLAH, da kuma kalman ALLAH, da kuma Ruhun ALLAH, Toh, kun gan kalmomin nan su na nufa wai da Yesu Christi, da kuma Ruhu mai tsarki, duka na ALLAH ne, wato su halitan ALLAH ne, kuma duk hidiman su wa ALLAH ne, wato su manzanni ne wa ALLAH.
Kalman nan (alloli uku) bisa tunanin mutum ne. Ni ina iya amfani da Kalma alloli uku bisa na gane aikin su da kasancewan su. Ku gane; An kira, Alloli uku domin su ne uku ma su sugabancin duka duniya da Halita; ALLAH ne ya na doki kudiri, sannan sai ya gaya ma kalman sa Yesu Christi, sannan sai kalman nan ya gaya ma Ruhu mai sarki (domin shi ne ke kasancewa a cikin halitan ALLAH domin ya ba mu shaidan ALLAH ta wurin kalman ko halin sa, wato Yesu kenan) domin sauran halita su yi shaidan kalman. Dukan halita su na bayyana Yesu Christi ne ta hali, ta wurin tunani ta Ruhu mai tsarki, kuma ta hakan ne ALLAH ya yi nufi-domin mu zo ga Kaman daidai da shi. Su ne su na shugabacin mu ama su na yi bisa nufin ALLAH ne kuma ga girmama ALLAH ne.
CETON MU.
Ceto shi ne lokacin da mun ji kalman ALLAH dinan daga wurin kalman, wato Yesu Christi da kansa domin mu bayyana, ba ta Ruhu ba. Domin mun ki karbi tunanin Ruhu yayan da ba ta je daidai da dabarun mu ba. Kadda ku manta wai Yesu bisa Kalman ALLAH ko halin ALLAH ne ya halice mu ta cikin sa ko ta halin sa sannan ya ba mu halin nan ta Ruhu domin mu bayyana sa ta wurin tunanin mu a ayukokin mu.
Ama, da Kalman ALLAH wato Yesu, da kuma tunanin ALLAH wato Ruhu mai tsarki, duka su na ji daga wurin ALLAH ne sanan sai su aikata a cikin mu, sanan sai mu ma mu aikata ma junan mu da sauran halitan.
Toh rashin shaida ALLAH ne ta warin Ruhu mai tsarki ya kawo ga adinin nauyi na yan Israela da yanzu kuma Musulunci ta tayas. ALLAH kauna ne kuma hutu ne ma halitatun sa, kuma shaidan da ya ke so mu yi kenan. Ama su, sai sun ba ma mutani na su tunanin, wato ganin su abin da ALLAH ya ke. Toh a yin haka, sun kuma ba ma mutani kansune ba ALLAH ba. Toh ceton mu yayan da Yesu ya zo bisa kalman ALLAH, domin ya gaya ma na bayannuwar kansa da kuma Ruhu mai tsarki, ta yanda ALLAH na bukatan mu mu yi rayuwa Kaman yara ko yan tunkiya (shaida na na Yesu Christi kenan), wato masu kwanciyan rai (Matthew 11:28-29), wato mu daina halita ganin mu bisa abun da ALLAH ya ke.
Da kalman ALLAH, wato Yesu Christi da kuma tunanin ALLAH, wato Ruhu mai tsarki, su ne ma su sugabanci duniya a madadin ALLAH, kuma su ne ma su shigar da halita ga sujada ga ALLAH, domin su ne sun fi kusa da ALLAH, kuma su ne sun fi sanin ALLAH. Duka sanin ALLAH’n mu ta wurin su ne. Su su ke ba mu abun da ALLAH yake, su su ke ba mu shaidan ALLAH. In ba ta wurin su ba, ba mu da sanin ALLAH, kuma ba mu da zuwan kusa da ALLAH.
ALLAH ne ke karbi duka sujada, ama sai ta wurin yesu. Duk sujadan da bai kasance da niya mai kyau ba, ba zai samu zuwa wurin ALLAH ba.
Yesu ya fita ne daga wurin ALLAH, wato ALLAH ya fitad da shi ta wurin kalman sa domin ya jagorance duniya (John 1:1-2 16:27-28). Yesu abin da ALLAH ya ke ne, ama Yesu kuma ba ALLAH ba. Da Yesu da kuma Ruhu suna ji daga wurin ALLAH ne kamin su aikata, ama su ma suna iya aikata na kansu domin su na da allantaka su ma. Su Alloli ne, Kaman da ALLAH, ta yanda abun halitan su ruhu ne ba kasa ba.
SHAIDAN YESU BISA SHI MA ALLAH NE.
Shaidan da mu ka bayyar da cewa Yesu Allah ne, ba wai haka kowai ne mun rubuta ba. Ama Ruhu ne na ba mu shaidan mutumin Yesu Christi. Abun sai ya kira mu ne ya kuma gaya ma na; mutum din can dan kun gan sa, shine mahalicin ku da kuma wanda ya halice duniya, mutum din can da ba shi da gida ko wani abu, duniya ta zo daga wurin sa ne, mutum dinnan da kana mari, shi ya halice ka. Eh, domin mu bayyar da shaida wai Yesu ba mutum kowai ba ne, kuma asalin sa ko farkon sa na allantaka ne. A duniyan nan, ya kasence mutum, ama farkon sa ba’a duniyan nan ba ne ama a mulkin sama ne, kuma farkon sa tare da ALLAH ne. Kuma Ruhu mai tsarki ne ya bayyar da sanin nan, domin mu zo ga gane da kuma karbi ceton mu.
ALLAH ne ya halice sa ko ya fitar da shi bisa kalman sa domin ya jagorance duniya. An halice sa bisa kalman ALLAH ma ne ne domin mu zo ga sanin ALLAH ta wurin sa, kuma mu zo ga rayuwa ta wurin dokokin da zai ba mu bisa mai sanin ALLAH ko mai kama da ALLAH. ALLAH ya fitar da shi ma na ne ama ba ma kansa ba ne.
Shi ne mai zuwan aikan ALLAH. Misali shi ne; da yayin da ALLAH ya yi niyan cece mu, mun gan Yesu Christi ne mai ceton. Kuma idan ALLAH zai warkas da mu, Yesu ne likitan. Da kuma yanda ALLAH ya so ya yi halita, kuma Yesu ne ya yi halitan. Duka ma ALLAH ne, kuma duka su na sujada ma ALLAH ne, ama ta wurin zuciyan Yesu Christi.
ADINI/SHAIDAN ALLAH TA WURIN DOKOKIN SA.
Shi Allah mai kyau ne, kuma ya halice mu domin mu zo mu yi shaidan kyau dinan ne. A dukan dokokin sa ko kuma hanyoyin sa, a kwai shaidan su. Dalilin halitan mu kenan, domin mutum ya zo ga dandana wannan halin ALLAH din. Ba zamu bi mu kira mutum dan bauta Kaman ALLAH ba shi da kyau ba. Shi ya na da kyau kuma kamata mu zo ga bin sa ta wurin zabi da kuma shaidan sa, ama ba ta wurin dole ba. Ba zamu bi mu kira kiyayye dokokin ALLAH yin bauta ba, domin dokokin nan suna da kyau.
Ama dai Musulunci, yayan da su zaba su kiyaye dokokin hukuncin kisa nay an israelawa am aba na Yesu ba, dalilin da suna ganin adinin Kaman halin bauta ne. Ama mu, ta wurin Yesu Christi, muna shaidan dokokin ALLAH ta wurin da suna da kyau.
Kalman da wai mutum abun bauta ne ya kasance da alhakin laifi da wai Muhammed ya san da cewa dokokin hukuncin kisa na yan israelawa mumuna ne, ama shi ya dauke su ayoyi ne, wato abun da ALLAH ya nufa kenan, dalilin da ya koya ma Musulami da wai su yan bauta ne kuma dalilin halitan su kenan.
Kuma a hadith dabam dabam aka gaya mana yanda Muhammed yakan yafe aikata hukuncin kisa a wayensu lokatai. Toh sa’alin da doka halin ALLAH ne, kuma musulunci ta amince da wai dokokin hukuncin kisa, halin ALLAH ne, kamata a ce wai ‘manzon ALLAH’ ya nuna iko akan wayensu dokokin nan a wayensu lokatai?
Toh dalilin da akwai tsattsauran ra’ayi kenan yau a Musulunci, dalilin da su sun kasance da tunanin da wai ALLAH ba ya canzawa, dalilin da sun kasance a aikata dokokin kisan nan kenan.
Kuma tunanin da wai ALLAH ba ya canzawa ne ya kawo yanda Muhammed ya ambata da wai Yesu ya zo ya cika dokokin hukuncin kisa na Torah. Ama Yesu mana bisa kalman gaskiya, ya kuma nuna ma na da cewa dokokin kisan nan tunanin mutum ne, ama ba ayoyi daga wurin ALLAH ba ne.
Ama kuma sai Musulunci wai sai ta gaya ma musulmai da wai idan sun aikata zunubi, sai kuma su ki amince da zunubin nan domin kadda a yi musu horo. Toh, wato ALLAH ya bayyar da dokokin horo ko hukuncin kisa a aikata, sai kuma Musulunci ta halita wani tsari ta yanda ba za aikata wanan hukuncin kisa din ba, kuma a sunan ALLAH? Toh wanan mun zama da ALLAH makaho kenan? Da ya bayyar da doka, sai kuma shi ne ya bayyar da hanyan da ba za kiyaye dokokin nan ba.
Toh wato yanzu a Musulunci, ba tuba kenan? Muna tuba ga ALLAH ne domin idan mun karye doka, mun ki ALLAH ne. Toh idan mutum ya na iya canza amincin zunubi da wai shi bai aikata zunubin ba, wanan ba shi ne mun amince da wai ba zunubi ba? Wanan ba halin masu rashin imani ba?
Kuma repotu ya ce wai Mohammed ya gaya ma mutani da wai idan sun yi zunubi, kadda su gaya ma sa, dalilin da wai zai aikata hukuncin kisan a kan su, kuma wai shi din ne kuma na gaya ma mutani wai su kawo kansu domin a aikata masu hukuncin kisa a sunan tuba. Kawrai, Muhammed ya san da cewa hukuncin kisa ba kyau, ama dalilin me ne ya ambata da wai Yesu ne kalman gaskiya, sai kuma ya ki karbi dokokin gafaran da Yesu ya kawo?
YESU BISA ZUCIYAN MU.
Yesu Christi ne kalman ALLAH, shi ne zuciyan da mu na yin ayukokin mu ta. Shi ne zuciyan ganewan mu, kuma shi kauna ne, kuma shi hutu ne, kuma shi rai ne, kuma shi sujada ne, kuma shi tsarki ne, kuma shi mai rashin alhakin laifi ne.
Toh, kamata mu yi shaidan kalmomin nan ma kanmu da kuma ma junan mu, da kuma ma sauran halitatu.
Kuma shi bisa Kalman ALLAH, tah wurin sa ne mu na sanin kan mu, wato halin mu, wato abun da ya kamata mu ke, da abun da ya kamata mu na yi. Shi ne kalman, sai kuma mu ne jikin sa. Mu, na mu shi ne mu yi shaidan kalmomin nan domin mu kasance a tarayya da ALLAH.
Wannan abun farin ciki ne ma na domin da ba don kasancewan sa ba, ba yanda mutum zai iya samu tarayya da ALLAH, domin mutum bai san ALLAH ba. Kuma da ba Yesu ba, da sujadan mu wa ALLAH zai kasance da nauyi sosai kaman yanda Israelawa da kuma ku, wato Musulunci, sun kasance. Ama domin shi ne sujadan mu da ALLAH, ta wurin shi ne ya halice mu, kuma shi ne kalman ALLAH ko halin ALLAH, sanan ya zo ya gaya ma na cewa, duka sujadan an ma na ko ta wurin dokokin ALLAH, na mu kowai mu kiyayye su ne domin mu zo ka tarayya da ALLAH.
Yesu ya zo domin yancin mutum ne, ba domin ya zama da mu yan bauta ba. Shi a zuwan sa bai dauki allantkan mu ba, ama ya mayas da shi ne, ta wurin iya nuna gafara. Kuma a yayyan da adini za sa mu mu shiga halin bauta, ba shaidan bautan da mu ke yi, shi ya kawo yanci ma kowa, wato, kowa ma ya na iya kasance da na sa adinin, ama dai kadda ta zama da nauyi a kan ka.
Ba mua faranta zuciyan ALLAH idan wai dukan mu mun kasance da hali daya ga ALLAH. Ama sai kowa ma ya kasance da na sa halin ga ALLAH. Idan ka gan cewa daukaka ALLAH ya na da kyau, sanan na ka shi ne ka ba zuciyan nan ma mutum domin su ma su daukaka ALLAH ta na su hanyan, ama ba wai za ka ba su na ka hanyar ne wai su daukaka ALLAH ta shi ba, toh ka kuma sa kan ka ne hanyar ceto.
Toh kun gan a yau, Musulunci (wato masu aikata Musulnci) ba ta san ALLAH ko ba, ta san Muhammed ne domin dukan abun da ta na yi, ya zo da abun da Mohammed ne ya yi. Duk ku na kokoyon Muhammed ne, ama ba wai kuna sujada ma ALLAH ba ne. Muhammed sai ya dauki yancin mutani gabaki daya ga bauta ma ALLAH ta hanyar sa. Kamata da shi zai shigad’da mutani ga rayuwan daukaka ALLAH, ama ba wai zai ba ma mutani wannan halin daukaka ALLAH, ko kuma kalmomin da za su ambata a adu’a ko girmama ALLAH.
Abun kamar Baban gida ne, Sanan da ya tashi da safe sai ya warkas da kowa ma adu’a. Toh, da an kasance ma adua din nan, sai an samu ma su barci, dalilin da an tashe su ne daga barci ma adua’n. Toh, na sa ganin, wato baban gidan shi ne shi ya yi daidai. Ama ma ALLAH, SHI bai damu da lokacin tashiwan wani ba, ama dai sanan da mun tashi a lokoci dabam dabam, shi dai ya gan kowa a na sa lokacin na bauta ma sa, wato kowa ta wurin hanyar sa da ta kuma na sa kalman. Toh a haka ne yafi murna, domin ya gan mutani dabam a lokaci dabam, da yare dabam ama su na shaidan Ruhun sa, su na girmama shi da yancin su, su na kuma yin ma sa sujada ta wurin zabi.
Aikin shugaba shi ne ya dinga sa soron ALLAH da kuma kaunan ALLAH da kuma tunashin ALLAH a cikin zuciyan mutanin sa.
A TAKAICE.
Toh mun kuma gan da cewa ba zai iya faru wai wani yayi shaidan dukan adini guda uku ba, domin dokokin da halayen sun bambanta. Sa’alin da Muhammed ya amince wai Yesu ne kalman gaskiya, dalilin me ne ya kuma waye da adinin isaraelawa? Da Yesu ya zo ya cika adinin su israelawa, da za samu adinin masu bin Yesu ne?
Toh a haka mun gan da cewa akwai babban masala a kalman da wai Muhammed (da muslulunci) ya zo ga shaidan adinin israelawa da kuma adinin masu bin Yesu, sai kuma ya halita na sa. Wato Musulunci yanzu cikan adinin yan isaraelwa da adinin masu bin Yesu ne ko ita ma adinin kanta ne? Toh yanzu musulunci ne halin adinin yan Israelawa da kuma adinin yan masu bin Yesu? Sanan kuma me ne gudan halin adini guda biyu dinan a jikin mutum?
SHAIDA NA AKAN MUSULUNCI.
Sannan kuma Yesu ya buda mun zuciyan sa a kan Musulunci, ta yanda ALLAH ya na jin kishin sadaukarwa na su ma dokokin Muhammed da kuma ba gaskiya ba. Shi ne (Yesu) Gaskiya kuma kalmomin sa ne gaskiya ama sai Mohammed ya ba ma mutani wayensu kalmomi. Kalman sa (Yesu) ne hutu ne (Matthew 11:28), ama sai Muhammed ya ba ma mutani kalmomin nauyi. Kalman sa ne yanci, ama sai Muhammed ya ba ma mutani kangin bauta. Kalman sa ne kauna, ama sai Muhammed ya ba ma mutani ramako. Kalman sa ne ya zamar da mutum mai rashin alhakin laifi, ama kalmomin Mohammed ne ya zamar da mutani ma su alhakin laifi. Kalmomin sa ceto ne, ama kalmomin Muhammed na kai mutum ga hallaka. Har Kuma ALLAH ya kasance da nadama ta yanda Muhammed ya yaudare Musulmai a kan sa. Bai damu a kan ayukokin su ba sai dai a kan yanda suka mutu wa kalmomin Muhammed. Kwarai, ya na bukatan sadaukarwa na su, kuma wanan zai samu.
Ama mutanin nan;
- Ba swa caje Quran, ama sai aikata kalmomin domin aka kira su yan bayi.
- Kuma wai dokokin su ya ce ido ma ido, hanci ma hanci, ama a hakan sun kuma taru (ma ALLAH) fiye da mu (Masu bin Yesu) wanda dokan mu ya ce kadda muyi ma juna laifi ta zuciyan kauna. Dokan su ya ce su yi ta durkusawa wa ALLAH a sujada kuma har son biyar a rana, ama na mu ya kawo mana yanci ne. Ama sai kuma mu (Masu bin Yesu) muna samu damuwa da junan mu, kuma mun zama yan iska da yancin da Yesu ya kawo mana.
Yanda na fada, ALLAH bai damu da ayukokin ku ba, shi ya damu da sadaukarwa na ku ne ma dokokin Muhammed wanda wai aka gaya maku wai shi ne.
Kwarai Wayannan mutanin ALLAH ne, kuma mutanin Yesu ne, kuma zai yi fada ma mutanninsa nan wanda aka yaudare su a kan sa. Domin ba su fahimtar dokan Yesu da ya ce wai idan aka mare ka a kumatu daya sai ka juya dayan a mara ba, ama wannan ba ainayin bayannan Yesu ma masu bin sa ba ne. Ama wurin da mutum biyu sun kasance a cikin sunan sa (Yesu), doka na kauna na kan su, kuma ba wanda zai ji ma wani. (John 13:34-35, 13:14)
Musulunci ta kasance da tsoron ALLAH, ama ba a fiskance ALLAH daidai a adinin ba. Doka na kadda a yi ramako doka ne na kawo salama, kuma wanda aka yi ma su laifi har sun yi hakuri domin salama, wayenan ne yan ragon hadaya da ya kawo ga salama, kuma su ne mutanin ALLAH. Kuma ta yanda doka halin ALLAH ne, idan ka yi ramako, toh kai ma ka karya dokan kenan.
- Kuma da kyar ka samu Musulmace da wai ta raina maigidan ta dalilin da wai shi ba mai kudi ba ne. Matan ba swa taba konlon mazajen su ta bisa abubuwan da suna da shi. Girman na miji a Musulunci na nan an kafa ko, ba wani shaka konda ya na wane irin aiki ne. Dalilin da Musulmai suna nan a tare domin su ba ma su niman kan su a kayan duniya ba ne, domin kayan duniya ne na kawo ga bambamci da kuma nisa sakanin mutani konda adinin su daya ne. Su ne zan ce da su wai suna cikin hutu domin ba swa cikin rayuwan tara su tarkace duniya.
- Yayan mu yau sun shiga aikata ayukan duhu da iskanci domin su yi kudi, Ama su (Musulmi) sun kasance a cikin rashi, ama domin imanin su. Mutanin nan ba swa dauki ayukan kwarewa na mu, wanda yana iya sa mutum ya juya bayan sa ma danwan sa dalilin da wai ‘halin aikin kenan’. Ba swa shiga irin aikin da zai sa su ga iskanci, Aama sun kasance a rayuwan hali daya- ta yanda ya kamata. Shaitan ne ya kawo irin aiki na duniya da ba ya girmama ALLAH sanan ya na rudin mutani da kudi a ayukkokin nan, duk domin ya sa ma su zunubi. Sanan kuma sai ana samu masu bin Yesu ne a irin wanan wuraren.
- Quran ne na sugabanci a kasacen Musulmi. Da mata, da yara, da maigida, duk suna bin sugabancin Quran ne. Kuma na miji ba ya taba rayuwa a wajen Quran domin shi ne na miji, ama kuma shi ne na farko mai kiyayye dokokin nan, kuma yanda Yesu ya shaida mun aikin na miji a duniya, shine ya gan da cewa ana biyayya ga dokokin ALLAH a duk wurin da ya shiga.
- Mutanin nan suna iya yadda da wayensu gaskiya da ke nan a fili, Kaman zubar da ciki zunubi ne. Su ne su na rayuwan rashin kai ta yanda ba swa niman riba a kasuwancin su. Ama sai mu ne da muna da kalman gaskiya na ALLAH, ama sai shaitan ya yaudare mu ga yin rayuwa na kai, da kuma rayuwa Kaman wanda ba swa bi. ALLAH tsarki ne, kuma Yesu ya kasance a duniyan nan ta rayuwan tsarki ne, kuma kamata mu masu bin sa mu cigaba a tsarki ne, domin kuma ba mai ganin ALLAH a rashin tsarki, ama kuma sai mu ne mun kasance a rayuwan kazamta.
Abun sanin su, wato abun da na fadin su, kuma halin su, a kasashen su shine ALLAH. ALLAH da sujada ne abun wayin kowanen su. Ama abun sanin mu ba ALLAH ba, mazajen mu ba swa dauki kalman ALLAH bisa abun sanin su, dalilin da yaran mu suna iya girma su zama yan iska a angwanin mu da akwai eklesioyi dayawa. Ama su, mutumin ALLAH ne shine shaidan su, kuma dalilin da yaran su ba swa girma su nima ko san imanin su da kansu ba (konda ba kalman gaskiya bane suna shaida), domin ya nan a bayane, halin kowa ne.
Eh, mu ne (Masu bin Yesu) da bishara da kuma kalman gaskiya, ama musulunci-ta halaye dayawa; na rashin rayuwan kai, da tsoron ALLAH, da sujada, da zaman tare, da hutu daga rayuwan tarkace na duniya, sun fi mu shaidan Yesu Christi. Musulunci na yau ta na cikin Yesu Christi a ta wurare dayawa, kuma na bayar da gaskiya wai ba da dadewa ba, zaman su a cikin Yesu Christi bisa kalman gaskiya zai cika.
ALLAH bai ki yanayin sujadan ku ba, kuma kwarai ya na da kyau, ama dai idan ya kasance da nauyi a kan ka, ko ka dauke shi bisa hanyar ceto fiye da dokokin sa, toh dole ne ALLAH ya damu, domin shi bai tambaya wanan irin sujada daga wurin mutum ba, kuma shi ba nauyi ba ne a kan mu. Kadda ku daina sujdan ku, ama kadda ya zamar da ku yan bayi, domin dukan sujadan mu ba ya kara ma ALLAH komai.
YESU NE RAINON BANGASKIYAN ALLAH.
ALLAH ya ba dukan hukunci ma sa (Yesu) (John 5:22) dalilin da shi ne ya yi shaidan rayuwan mu ma ALLAH. Da ALLAH ya so ya bi na tsarkin sa ne, toh da ba mutum mai rai yanzu, ama ALLAH ya bi na rayuwan bangaskiya wanda Yesu ya kasance a ciki.
Wato yanzu, rayuwan Yesu ne ceto. Duk abin da ba shi ba, wato duk halin da bai bayanna a lokacin sa a duniyan nan ba, zai zo ga hallaka. Ma na ne yanzu, mu gyara zaman mu, da halayen mu, su je daidai da na Yesu, domin duk abin da ba halin shi ba, zai je wuta ne.
Toh ace ba mu yi rayuwan tsarkin ba, sanan kuma za ce wai rayuwan bangaskiyan ma ya gagare mu? Ana iya cece irin wanan mutanin? Su kuma sake zamar da sabon duniyan Kaman wanan da irin mumunan halin su? Ai ALLAH ba zai sha wahala son biyu ba. Duk wani mumunar abun da ba Yesu ba, zai zo ga hallaka ne.
Domin da ALLAH bai zo ga rage tsarikin sa zuwa bangaskiya a cikin Yesu Christi ba, da wane mutum ne zai tsira? Ama shaitan ne ya so ga hallakan mu, bayyan da ya rasa ta yanda Yesu yam utu ba zunubi domin musun sa da cewa mutum ba zai iya rayuwan tsarki ba, sai ya je ya halite mana wani rayuwan da ba za mu gane har ga aikata kalmomin bangaskiyan nan ba. Toh mun gan ya yi dai dai mu karbi kudi daga mutanin da basu da lafiya? Mene bayannan Yesu bisa kauna da mai tausayi idan muna karbin kudi a wurin mutanin da kamata mu bayanna masu dokokin ALLAH? A wane lokaci ne kamata ka bayanna wannan kauna din? Gabaki daya, rayuwan kudi da rayuwan kai da rayuwan kwarewa duk hanyoyi ne da shaitan ya na so ya yaudare mutani zuwa wuta.
SANIN YESU.
Sanin mutumin Yesu ba’a karatu ne kowai ba. Sanin Yesu a shaida ne. Idan kalman gafara ne, toh ba mana mu san kalman gafara ba ne kowai, mana ne mu aikata domin mu zo ga samun dandanon da kuma sanin kalman.
Toh kun gan, bisa irin duniyan da mu ke ciki, masu bin yesu ma basu da shaidan Yesu Christi ta dokokin sa, domin su ma suna da bukatu.
Yesu bai zo domin mu dinga girmama shi ko halin sa ba. Ya zo domin mu copa na shi ne ga samun ceto. Sani, wato ta wurin kalmomi ba ceto ba ne. Sani ta wurin dandano ne ceto, domin Yesu Christi kenan, wato ita kalman da bayas.
Eklisia na litaffi sun kasance da shaidan Yesu ne bisa mutum da bai yi rayuwan kai ba, ta wurin Yesu Christi (Act 4:31-32), dalilin da sun iya kasance tare kenan. Ama mun da wai muna bin Yesu, ba mu da Ruhu mai tsarki da zai yi mana shaidan mutumin Yesu Christi din nan. Mu na da sanin abun da eklisian Yesu kamata ta ke, ama rayuwan kai da shaitan ya sa mu a ciki na hana mu kasance a tare.
MUSULUNCI, ADININ LOJIK.
Musulunci, kamar adinin Israelawa ta nuna da cewa ita adinin ‘ganin mutum da kuma tunanin mutum’ ne. Toh kuma mun gan da cewa ALLAH ba mutum ba ne da wai ganin mu da tunanin mu za su faranta zuciyan sa. Ko akwai dalilin da ALLAH ya zabi ya gafarta ma na zunuban mu ne, da ba hallaka ba? Kuma akwai dalilin da mu ma kamata mu gafarta laifofin da an ma na? Mun gan da cewa dalilin nan, wato kauna ba tunanin mutum ba ne, tunanin ALLAH ne da ya so mutum ya aikata. Mutum ba ya iya halita ko sanin dalilan ALLAH, ama mu dai shaidan mu shi ne dokokin su na koshiyar da tunanin mu, ta yanda mu na gane niyan su.
Gani da tunanin mutum ne ne ya kawo da wai Yesu ba yaron ALLAH ba ne.
Gani da tunanin mutum ne ya kawo ga hukuncin kisa bisa wai tsarin dokoki na ALLAH.
Gani da tunanin mutum ne ya kawo ga wai ALLAH ba ya cin abinci.
Gani da tunanin mutum ne ya kawo ga wai Yesu ba Allah ba ne ta wurin da wai ya na da mama.
Gani da tunanin mutum ne ya kawo ga kwadin ALLAH ta ayokokin mu.
Gani da tunanin mutum ne ya kawo ga wai ALLAH ba shi da dai dai, domin ALLAH bai taba gaya ma na wai ya na da daidai ba. Kalman can kamata Musulunci ta gaya ma wanda sun ce wai ALLAH na da daidai ne, ama ba wai za su yi sujada ma ALLAH da kalman ba.
Gabaki daya gani da tunanin mutum ne ke kawo ga adini. Mu yi hankali, mu yi rayuwa ta saurara, ALLAH ba mutum ba ne; hanyoyin sa dabam ne da na mu, ganin sa dabam ne da na mu.
Ni na kuma bayyad da aika na; Ku saurara ku sami ceto, Yesu ne Almasihu kuma ta wurin sa ne kowai ana sami ceto. ALLAH ya albarkace ku.
AYOYI MASU ALAKA (AMA SUN KASANCE A TURANCI)
FAHIMTAR ZUWAN YESU CHRISTI;
https://christmyword.home.blog/2020/05/12/understanding-the-coming-of-christ/
RAYUWAN YESU KISHIN MUTUWAN SA BISA CETO/ DAN TUNKIYAN BISA MAI RASHIN ALHAKIN LAIFI; YANDA YESU YA NA DAUKI ZUNUBAI’N MU;
https://christmyword.home.blog/2020/09/01/the-life-of-christ-vs-the-cross-the-person-of-moses/
FAHIMTAR WAI GICIYE ALHAKIN ZUNUBI NE/ ANABAWA BISA AINAYIN MUTUMIN ALLAH DAGA ALLAH NA DOKA;
https://christmyword.home.blog/2020/07/30/tesimony-and-summary-of-the-prophets-on-sacrifices-christ-to-us/
RIKITAWA A KAN KALMA DAN TUNKIYA TSAKANIN YAHUDAWA DA MASU BIN YESU KUMA YANDA TA SHAFI MUSULUNCI DA KUMA DUNIYA;
https://christmyword.home.blog/2020/09/28/controversy-over-the-word-lamb-between-judaism-and-christianity-and-how-it-has-affected-islam/
ku dubi christmyword.home.blog domin ku gan dukan ayoyin da kuma hurraruka. Ku saurara ku sami ceto, ALLAH YA LURA DA KU.